✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Wa Kishiyar ASUU Rajista

Gwamnatin tarayya ta gabatar da takardun shaidar rajista ga wasu sabbin kungiyoyin malaman jami’a biyu. Kungiyoyin sun hada da ta Malaman Sashin Nazarin Likitanci da…

Gwamnatin tarayya ta gabatar da takardun shaidar rajista ga wasu sabbin kungiyoyin malaman jami’a biyu.

Kungiyoyin sun hada da ta Malaman Sashin Nazarin Likitanci da Lura da Hakori (NAMDA), da kuma ta Gamayyar Malaman Jami’o’in Najeriya (CONUA).

Ministan Kwadago da Ayyuka, Chris Ngige ne ya gabatar da takardar shaidar ga kungiyoyin a ranar Talata a Abuja.

Wannan dai na daga cikin kokarin gwamnatin na kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke yi na tsawom watanni takwas.

“Wadannan kungiyoyin za su yi aiki kafada da kafada ne da ASUU a jami’o’in Najeriya,” in ji Ngige.

Sai dai ya ja hankalinsu da kada su tsoma baki cikin harkokin gudanarwar jami’o’in.

Sabuwar Kungiyar Malaman Jami’o’in ta CONUA dai ta fara yunkurin samun rajistar ne tun a shekarar 2018.

Kungiyar karkashin jagorancin Niyi Sunmonu, wani malami a Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), ta jima tana nesanta kanta daga duk wani yajin aikin da ASUU ta kaddamar yi tun da jimawa.