✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomi 3

Dokar ta shafi kanana hukumomin Bukkuyum, Gummi da Anka, tare da rufe kasuwanni da manyan hanyoyi

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya dokar hana fita a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi sakamakon dawowar hare-haren ’yan bindiga.

A safiyar Juma’a gwamnatin jihar ta sanar da hana fita gaba daya a wasu manyan garuruwa tare da rufe kasuwanni da manyan hanyoyi, ta hannun Kwamishinan Yada Larabanta jihar, Ibrahim Dosara.

Ya sanar cewa, “Gwmanati ta rufe manyan garuwa tara domin dakile hare-haren ta’addandi da aka samu karuwarsu a wadannan wuraren.

“Garuruwan su ne Yarkofoji, Birnin Tudu, Rini, Gora Namaye, Janbako, Faru, Kaya, Boko da kuma Mada.

“Gwamnati ta kuma rufe kasuwannin Danjibga da Bagega da kuma hanyar Colony zuwa Lambar Boko, hanyar Bakura zuwa Lambar Damri da kuma hanyar Mayanchi zuwa Daki Takwas zuwa Gummi.

“Sauran hanyoyin da aka rufe su ne na Daki Takwas zuwa Zuru Road, Kucheri-Bawaganga–Wanke Road, Magami zuwa Dangulbi da kuma hanyar Gusau zuwa Magami.”

Ya ce, “An dauki matakin ne domi bai wa jami’an tsaro damar fatattakar bata-garin daga yankununan.”

Gwamnan Jihar, Muhammad Matawalle ya kuma dakatar da duk tarukan da jam’iyyarsa ta APC za ta gudanar a matsayin nuna damuwa kan halin da yankunan suke ciki.