✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Habasha: Yaki ya sake barkewa a yankin Tigray

Bayan wata daya, an ci gaba da yaki tsakanin sojojin da maykan kungiyar TPLF.

Yaki ya sake barkewa ranar Laraba a yankin Afar na Arewacin kasar Habasha bayan kusan wata guda.

Tun a ranar Talata aka fara samun rahotannin yake-yake a garin Awra da ke yankin Fenti, inda ake zargin ’yan tawayen Tigray daga kungiyar TPLF sun harbe fararen hula da makamai atilari.

Rahotaonnin sun bullo ne daga kungiyoyin jinkai, sai dai ba a samu tabbaci ba daga hukumonin yankin Afar, domin jin ta bakinsu.

Kakakin mayakan TPLF, Getachew Reda ya tabbatar da dawowar yaki a yankin Afar, amma ya musanta cewa kungiyar ta kashe fararen hula da manyan makamai.

Ya ce, “Mayakan abokan gaba sun tarwatse a yankin Afar,” a yayin da yake kwatanta abin da ke faruwa a yankin iyakar da ke tsakanin yankunan Afar da Amhara.

“Babu ruwanmu da fararen hula, zargin amfani da bindigogin atilari  kuma labarin kanzon kurege ne domin bata mana suna,” inji shi.

Kusan mako guda ke na da ma’aikatan jinkai da ’yan tawayen Tigray ke zargin sojojin gwamnati Habasha da kai hare-hare da ke iya dawo da rikici a yankin Arewacin kasar.

Tun da farko dai gwamnatin kasar ta nuna akwai yiwuwar kai hare-haren, inda ofishin Fira Minista Abiy Ahmed ya ce “Nauyi ne kan gwamnati ta kare duk ’yan ksarta daga kowane irin ta’addnci.”

– ‘Karya shinge’ –

A watan Nuwamban 2020 ne fada ya fara barkewa a yankin Arewacin Tigray bayan Fira Minista Abiy ya tura sojoji sun tarwatsa mayakan TPLF, kungiyar da ta mamaye fagen siyasar kasar dab da hawansa mulki a 2018.

A lokacin, Abiy ya ce hakan da sojoji suka yi martani ne a kan  harin da mayakn suka kai wa sansanonin soji.

Cikin dan kankanin lokaci sojojin suka fatattaki TPLF daga yankunan Tigray, amma zuwa karshen watan Yuni, mayakan suka sake kwace yakunan, har da garin Mekele da ke zama hedikwatar yankin.

A watan Yuli TPLF ta dannan zuwa yankin Afar da Amhara masu makwabtaka da su, da sunan kokarin hana sojoji keta shingen kare yankin Tigray, yankin da Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasa akwai dubban mazanauna da ke cikin tsananin bukatar aminci da kayan agaji.

A watan Satumba TPLF ta sha kashi a yankin Afar, har ta janye domin mayar da hankali a wasu wurare ciki har da Amhara.

Tun a lokacin aka ji tsit a yankin Afar wanda yanzu shi ne cibiyar da mah’akatan jinkai ke iya shiga yankin Tigray.

A ranar Laraba, Getachew ya ce suna shirin kora sojojin su koma baya domin kar su shigo yankin Tigray.

– Neman tsagaita wuta –

Rikicin Tigray dai ya sa dangantaka ta sa yi tsami tsakanin gwamnatin Fira Minista Abiy Ahmed da kasashen duniya, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya.

Gwamnatin Amurka ta ce tana duba yiwuwar daukar matakan da suka dace, ciki har da yiwar sanya takunkumin tattalin arziki da kuma ganin an hukunta masu rura wautar fitinar da hana ayyukan jinkai.

A ranar Talata, kasashen Amurka da Farasa da Birtaniya da Jamus da Tarayyar Turai sun bukaci bangarorin da ke rikicin da su tsagaita wuta su hau teburin sulhu.

A wata sanarwa, Shugabar Hukumar Agaji ta Amurka (USAID), Samantha Power, ta roki gwamnatin kasar Habasha ta bude harkokin abki da sadarwa da sauran harkoki a yankin Tigray.

Ta ce Amurka da kawayenta na kokarin ci gaba da kai agaji ta sama a yakin daga Addis Ababa, baban birnin kasar Habasha.