✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe mutum 15 da raunata 42 a Neja

Rahotanni daga karamar hukumar Bida a jihar Neja na bayyana cewa, mummunan hadurra biyu na motoci ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 15 da raunata mutum…

Rahotanni daga karamar hukumar Bida a jihar Neja na bayyana cewa, mummunan hadurra biyu na motoci ya yi sanadiyyar rasuwar mutum 15 da raunata mutum 42.

Darakta Janar na hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Neja NSEMA, Alhaji Ahmed Ibrahim Inga ya tabbatarwa majiyarmu aukuwar hadari.

A cewar Alhaji Ahmed, hadarin farkon ya faru tsakanin wata tirela dauke da shanu da ke tafiya a hanyar Minna zuwa Bida, yayin da dayan kuma hadarin ya faru da wata tirela da ta dauko tumatir a hanyar Bida zuwa Mokwa duk a cikin jihar.