✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadarin mota ya kashe ’yan Najeriya 14,773 a cikin shekaru 3

An samu mutum fiye da dubu 100 da hadari ya ritsa da su cikin shekaru uku a Najeriya.

Mutum 106,256 ne a Najeriya hadurran mota suka ritsa da su a tsakanin watan Janairun 2019 zuwa Disambar 2021.

Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai mutum 14,773 da suka mutu a hadurra 31,116 da suka auku a tsawon wannan lokaci kamar yadda kididdigar da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) da kuma bayanan da Jaridar Aminiya ta tattaro suka nuna.

Alkaluman Hukumar FRSC sun bayyana adadin hadurran mota da suka auku a tsakanin watan Janairun 2019 zuwa Oktoban 2021, yayin da na Jaridar Aminiya suka tattaro alkaluman hadurran da suka auku daga watan Nuwamba zuwa Disambar 2021.

Baya ga mace-macen da aka samu, mutane 91,483 sun samu raunuka iri daban-daban a hadurran da aka samu tsawon wannan lokaci.

Alkaluman sun nuna cewa shekarar 2021 ce ta fi kowacce yawan hadurra idan an kwatanta da shekarun baya, inda aka samu aukuwar hadurra 10,637 da suka ritsa da mutum 35,791.

Daga cikin wannan adadi, mutum 5,101 sun riga mu gidan gaskiya yayin da mutum 30,690 suka sami raunuka iri-iri kuma mabanbanta girma.

Kididdigar ta nuna cewa Jihar Ogun ce ta fi kowacce hanyoyin masu hadari inda aka samu aukuwar hadurra 1,026 wanda shi ne adadi mafi yawa da aka samu a jiha daya a bana.

Haka kuma, alkaluman sun nuna cewa Jihar Bayelsa ce ke sahun gaba ta fuskar tituna masu aminci, inda aka samu aukuwar hadurra 40 kacal a bana.

A shekarar 2020 da ta gabata, hadurran ababen hawa 10,522 suka auku a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba, inda fashin baki ya nuna cewa mutum 4,794 sun mutu yayin da wasu 28,449 suka jikkata.

Sai kuma a shekarar da ta gabata kafinta, wato 2019, duk da cewa an samu karancin aukuwar hadurran ababen hawa da adadinsu ya kai 9,957 , sai dai an samu mutane mafi yawa da suka rasu wanda adadinsu ya kai 4,878.

Alkaluman sun nuna cewa mutum 32,344 ne suka jikkata a sakamakon hadurran da suka auku a shekarar 2019.

Jami’in wayar da kan al’umma na Hukumar FRSC, Bisi Kazeem ya alakaanta aukuwar hadurra da tarin dalilai ciki har da gudun wuce sa’a, karya dokokin hanya, matsalar ababen hawa, tuki cikin maye da kuma tukin ganganci.

A cewarsa, hukumar na kara fadada hanyoyin wayar da kan alumman domin sauya munanan halaye na tukin ababen hawa tare da bullo tsare-tsare masu nasaba da sakamako mai inganci.

Bisi ya ce hukumar ta mayar da hankali wajen rage aukuwar hadurra masu nasaba da gudun wuce sa’a wanda galibi shi ne musababbin hadurran da suka fi aukuwa a yanzu.