✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Duk da amfani da maganin hana daukar ciki, mai ’ya’ya 7 ta haifi ’yan 4

Hakan ga faru ne duk da yunkurinsu na dakatar da haihuwar

Ma’aurata masu ’ya’ya bakwai sun kara samun karuwar ’yan hudu duk da amfani da maganin hana daukar ciki ko tsarin iyali don dakatar da ci gaba da haihuwa.

Aminiya ta ruwaito cewa, mijin, mai suna Christopher Agbo da matarsa Mercy wadanda mazauna yankin Sabon-Tasha ne a Gwagwa cikin Babban Birnin Tarayya Abuja, sun samu karuwar ne a ranar Alhamis da ta gabata a wani asibiti mai zaman kansa da ke Kubwa.

Magidancin wanda dan asalin Jihar Binuwai ne ya bayyana cewa, bayan da suka samu haihuwar ’ya’ya biyar sai suka yanke shawarar dakatar da ci gaba da haihuwa haka nan, daga nan suka tafi asibiti matarsa ta shiga tsarin iyali inda aka saka mata roba a dantsenta .

Ya ce, “Bayan wata uku da saka mata robar, sai muka fahimci abin ba ya aiki yadda ya kamata, daga nan ne ta koma yin amfani da maganin hana daukar ciki.

“Amma duk da haka, bayan wani lokaci sai ga ciki, kuma da muka tafi asibiti aka gwada sai aka tabbatar mana cewa cikin na ’ya’ya hudu ne,” inji magidancin.

Ya kara da cewa, “Da tafiya ta yi tafiya, sai ga alamun nakuda sun bayyana a ranar Alhamis wanda hakan ya sa muka garzaya asibiti inda ta haifi ’ya’ya hudu da kanta ba tare da yi mata aiki ba.”

Da yake tsokaci game da lamarin, Shugaban asibitin da ya karbi haihuwar, Dokta Onogwu Joseph ya ce, “Ba ni da masaniya a kan ko matar ta yi amfani da abubuwan hana daukar ciki. Amma ina kyautata zaton inda a ce ta yi amfani da maganin yadda ya kamata da hakan ba ta kai su ga samun haihuwar ba.”