✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanifa: Matar Abdulmalik za ta yi wani jawabi a gaban kotu

Kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare Jamila kan taimaka wa mijinta bayan ya sato Hanifa

Kotu ta ba da umarnin tsare Jamila Muhammad Sani, matar malamin nan da ya sace dalibarsa, Hanifa Hanifa Abubakar mai shekara biyar, ya kuma kashe ta a Kano, a hannun ’yan sanda.

An gurfanar da matar Abdulmalik a gaban kotu ne a ranar Alhamis bisa zargin ta da boye marigayiya Hanifa a hannunta bayan mijinta, Abdulmalik Tanko, mamallakin Makarantar Noble Kids School, ya sato dalibar.

Mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya shaida wa kotu cewa Jamila wadda mata ce ga wanda ake zargi da sacewa tare da kisan Hanifa, ta taimaka masa wajen boye Hanifa a gidanta na tsawon kwana biyar.

“Ke Jamila Sani wacce a ranar 4 ga watan Disamba 2021 mijinki Abdulmalik Tanko ya kawo miki Hanifa Abubakar mai shekara biyar da kayan makaranta a jikinta; Kina sane da cewa mijin naki sato ta ya yi, amma kika karbe ta tare da ajiye ta a gidanki ba tare da kin sanar da kowa ba.”

Sai dai Jamila ta musanta zargin da ake mata na aikata laifin, wanda ya saba da sashe na 227 na Kundin Shari’a na Pinal Kod.

Ta kuma bukaci kotun ta ba ta dama domin ta yi wani jawabi, amma lauyan gwamnati ya nemi kotun da ta sa wata rana ta daban domin sake gurfanar da wacce ake zargi a gaban kotun.

Alkalin kotun Mai sharia Muhammad Jibrin ya amince da bukatar mai gabatar da kara inda ya sanya ranar 2 ga watan Fabrairu don sake gurfanar da matar ta Abdulmalik.

Haka kuma alkalin ya ba da umarnin a sake mayar da Jamila hannun ’yan sanda su ci gaba da tsare ta a maimakon gidan gyaran hali.