✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi 7 na magance matsalar warin jiki

Ga hanyoyin da zaku bi don rabuwa da warin jiki

Warin jiki na daya daga abubuwan da suke janyo tsana a tsakanin mutane. Musamman lokacin zafi idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana na tsawon lokaci sai a ji warin jiki na tashi.

Ana samun warin jikin ne saboda yanayin gari, a haifi mutum da shi ko kuma ta irin abincin da muke ci.

Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun guso sai an ji tashin tafarnuwar.

Don haka ne a yau na kawo muku hanyar da ita ce mafi sauki don magance wadannan matsaloli.

Turare: Yawan fesa turare na jiki ko na hamata na rage warin jiki. Amma yawan amfani da su na janyo kyenkyemi wanda zai sa kuraje fesowa.

Sabulu da ruwa: Hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce amfani da ruwa da sabulu don yin wanka kamar sau uku a rana kuma a dage da wanke lungun da ke janyo wari kamar su hamata da sauransu.

Tsabtatace riga: Kada a manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan kayan da yake sanyawa masu dauda ne to lallai ba zai rabu da warin jiki ba. Don haka ana son ana sa kaya masu tsabta musamman kayan da ake sanyawa a ciki kamar rigar nono da sauransu.

Amfani da alimun: Idan warin jiki ya kasance mai tsanani ne to sai a rika wanka da alimun domin rage warin.

Zuma: Idan an gama wanka za a iya zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi sannan a watsa a jiki hakan na rage warin jiki.

Shan ruwa: Domin rage warin jiki, a sha kofin ruwa daya da sassafe kafin a ci komai. Yin haka na rage warin jiki.

Amfani da ruwan rose (rose water): Za a iya diga ruwan rose a cikin ruwa kafin a yi wanka hakan na rage warin jiki da kuma dada wa jikin kamshi.