✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin bom ya kashe fasinjoji 9 a mota a Mali

’Yan sanda sun ce akalla mutum tara sun rasu a wani hari da aka kai wa wata bas a kasar Mali a ranar Alhamis.

’Yan sanda sun ce akalla mutum tara sun rasu a wani hari da aka kai wa wata bas a tsakiyar kasar Mali a ranar Alhamis.

Harin ya ritsa da bas din ne a hanyar Bandiagara zuwa Goundaka, a yankin Mopti a kasar da ke fama da hare-haren masu ikirarin Jihadi.

“Yanzu muka dawo daga kai gawarwaki tara asibiti, kuma ba mu kammala ba,” a cewar Moussa Housseyni, daga Kungiyar Matasan Bandiagara.

Wani jami’in dan sanda da ya nemi a boye sunansa ya ce akalla mutum 10 ne aka kashe, wasu da dama kuma sun samu raunuka a harin.

Kasar Mali ta jima ta na fama da hare-haren masu ikirarin jihadi, wadanda suka yi ajalin dubban rayukan fararen hula da jami’an tsaro baya ga wadanda suka rasa muhallansa.

Maharan kan yi amfani da nakiyoyi da abubuwan fashewa da suke hadawa su tayar daga nesa wajen kai hare-hare.

Wani rahoto na rundunar samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (MINUSMA) ya ce zuwa karshen watan Agusta, nakiyoyi sun kashe mutane 72, wadanda yawnacinsu sojojiji ne.