✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin kunar bakin wake ya yi ajalin mutum 52 a wurin taron Maulidi

Hukumomi sun saka dokar ta-ɓaci a yankin.

Akalla mutane 52 sun mutu a harin kunar bakin waken da aka kai kan dandazon masu taron Mauludi a lardin Bolichistan da ke Pakistan.

Lamarin ya faru ne a kusa da wani masallaci yayin da mutane suka taru don yin bikin tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) a wannan Juma’ar.

Majiyoyin labarai daga yankin na Bolichistan sun tabbatar da karuwar alkaluman a harin na  da aka kai gab da babban masallacin yankin Mastung wanda da farko ya kashe mutane 42 tare da jikkata mutane akalla 80 ciki har da wadanda ke cikin mawuyacin hali.

Karamin Ministan Lardin na Balochistan, Zubair Jamali, ya tabbatar da cewa harin ya rutsa da tarin mutane ciki har da kananan yara.

Rahotanni sun bayyana cewa dan kunar bakin waken ya yi damarar bom tare da shiga cikin dandazon mutanen da ke halartar taron Mauludin inda ya tayar da bom din gab da motar babban sufuritandan ‘yan sandan yankin da ke bayar da tsaro a wajen Nawaz Gishkori.

Hukumomi sun saka dokar ta-ɓaci, yayin da ake ci gaba da kai waɗanda suka jikkata asibitoci biyu mafiya kusa.

Bidiyon da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda masu bayar da agajin gaggawa da jama’ar yankin ke aikin ceto.

Har zuwa yanzu dai babu kungiyar da ta dauki alhakin harin na yau Juma’a, sai dai kungiyar IS ta yi kaurin suna wajen kai makamantan hare-haren yayinda cikin gaggawa kungiyar TTP ta nesanta kanta da harin.

Ko a watan Yulin da ya gabata, sai da wani harin ta’addanci ya hallaka sojojin Pakistan 12 a Lardin na Bolichistan kari kan kisan jami’an tsaro 9 cikin watan Maris duk dai a yankin mai fama da matsalar tsaro.