✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin makami mai linzami ya kashe mutum 17 a Ukraine

Akalla mutum 17 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai cikin dare a Zaporizhzhia da ke Kudu…

Akalla mutum 17 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani harin makami mai linzami da Rasha ta kai cikin dare a Zaporizhzhia da ke Kudu maso Gabashin Ukraine.

Anatoliy Kurtev, Sakataren Majalisar birnin Zaporizhzhia, ne ya bayyana hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Telegram.

Ya sanar cewa, bayan harin makami mai linzami a Zaporizhzhia, akalla gidaje 20 da kuma gine-ginen benaye kusan 50 sun lalace.

Haka kuma ya ce mutane 17 ne suka mutu ya zuwa yanzu sannan kuma an lalata cibiyoyin ilimi hudu.

Zelensky da jami’in yankin Oleksandr Starukh sun bayar da adadin wadanda suka mutu ya kai 12, yayin da na baya-bayan nan ya ce akwai yiwuwar wasu karin wadanda abin ya rutsa da su na karkashin baraguzan ginin yayin da aka kaddamar da aikin neman ceto.

Akalla mutane 17 ciki har da wani yaro ne suka mutu a yayin da wasu makamai masu linzami na Rasha bakwai suka afkawa Zaporizhzhia kafin wayewar gari a ranar Alhamis, kamar yadda hukumomin Ukraine suka sanar a wani adadi da aka yi wa kwaskwarima ranar Asabar.

Zaporizhzhia dai na kusa da fagen daga inda dakarun Kyiv ke kai wani gagarumin farmaki kan sojojin Rasha.

Manyan wuraren da ke da kamfanonin da ke karkashin ikon Ukraine yana cikin yankin Zaporizhzhia, wanda kuma ke da tashar nukiliyar da Rasha ta mamaye, inda aka yi ta luguden wuta.

Moscow ta yi ikirarin mamaye yankin duk da cewa dakarunta ba su da iko da shi baki daya.

Ukraine ta ce akalla mutane 30 ne suka mutu a makon da ya gabata, lokacin da aka kai har ikan wani ayarin motocin farar hula a yankin Zaporizhzhia alhakin da aka dora wa Moscow.

Rasha ta tsaurara tsaro a gadar da bam ya lalata

Rasha ta tsaurara tsaro a kan gadarta tilo da ke sada kasar da yankin Crimea da ta mamaye a 2014 bayan wani harin bam ya lalata wani bangare na gadar a ranar Asabar.

Shugaban Kasa Vladimir Putin ya umarci hukumar tsaro ta kasa wato Federal Security Service (FSB) ta karbe aikin kula da hanyar.

Harin na jiya ya kashe mutum uku wadanda masu bincike suka ce ana kyautata zaton suna cikin wata mota ne da ke kusa lokacin da motar da bam din ke ciki ta tarwatse a kan gadar.

A gefe guda kuma, masu ninkaya na Rasha sun soma cikakken bincike a kasan ruwa domin gano irin illar da fashewar da aka samu a kan gadar Kerch ta yi wa gadar wadda ke hade Crimea da Rasha.

Bangare guda na gadar ya rushe baki daya, haka kuma fashewar ta shafi layin dogon da ke saman gadar daga gefe inda har wani jirgin kasa na dakon mai ya kama da wuta.