✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin ’Yan bindiga: Saudiyya ta ba da tallafin abincin $1.2m a Zamfara

Cibiyar jin-kai da bayar da agaji ta Sarki Salman na kasar Saudiyya ta bayar da tallafin kayan abinci ga mutanen da harin ’yan bindiga ya…

Cibiyar jin-kai da bayar da agaji ta Sarki Salman na kasar Saudiyya ta bayar da tallafin kayan abinci ga mutanen da harin ’yan bindiga ya ritsa da su a Jihar Zamfara. 

Daraktan hukumar bayar da agaji na kasa (NEMA), Muhammadu Muhammed, ya bayyana wa taron manema ranar Juma’a a Gusau cewa za a raba abincin kimarsu ta kai Dala miliyan daya da dubu dari biyu ne ga akalla magidanta kimanin 8,725.

“Kowanne daga cikinsu ana sa ran zai karbi kayan da nauyinsu ya kai 59.8kg da suka hada da shinkafa da wake da tumaturin gwangwani da magi da man girki da kuma fulawa.

“Ana sa ran kayan za su kai ga mutanen da za su amfana don su samu su yi amfani da su a wannan lokaci na azumi,” a cewarsa.

Shugaban na NEMA ya yaba wa cibiyar ta Sarki Salman kan rabon kayan tallafin, yana mai cewa Najeriya tana farin ciki da maraba da irin wannan gudunmawa wadda cibiyar ta yi makamancinta a jihohin Borno da Yobe.

Kwamishiniyar Jjn-kai da bayar da agaji ta Jihar Zamfara, Faika Ahmed, wacce ta karbi kayan a madadin Gwamnatin Jihar, ta godewa NEMA da kuma cibiyar ta Sarki Salman kan bayar da kayan tallafin ga jama’ar Jihar.