Hisbah ta haramta casun sallah a Jigawa | Aminiya

Hisbah ta haramta casun sallah a Jigawa

    Abubakar Muhammad Usman

Hukumar Hisbah a Jihar Jigawa ta yi gargadi ga masu shirin shirya casu a lokacin bikin Sallah.

Hukumar ta ce za ta sa kafar wando daya da duk wanda ya shirya casu ko alfasha a lokacin bikin Sallah Karama, kamar yadda Shugabanta, Ibrahim Dahiru ya bayyana a garin Dutse.

“Muna amfani da wannan dama domin yin gargadi cewa jami’anmu za su cafke duk wanda ya aikata alfasha da sauran munanan dabi’u irin kidan DJ da rawa da sayarwa ko amfani da kayan wasan wuta.

“Kamar kowace shekara, wannan karon ma ba za mu yi kasa a guiwa ba wajen haramta wa matasa aikata munanan dabi’u, ciki har da kade-kade da raye-raye tsakanin maza da mata,” a cewarsa.

Hisbah ta yi wannan gargadi ne a wani yunkuri da ta kira na dakile munanan dabi’u a fadi  Jihar.