Hisbah za ta debi sabbin dakaru 3,100 a Kano | Aminiya

Hisbah za ta debi sabbin dakaru 3,100 a Kano

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje sanye da kayan Hisbah
Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje sanye da kayan Hisbah
    Sani Ibrahim Paki

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince wa Hukumar Hisbah ta Jihar ta debi sabbin dakaru 3,100 a Kananan Hukumomin Jihar 44.

Babban Kwamandan Hukumar a Jihar, Dokta Harun Ibn Sina ne ya bayyana hakan, kamar yadda Kakakin hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ya sanar.

Ibn Sina ya kuma ce kaso 80 cikin 100 na mutanen da za a diba za su kasance maza ne, sau kuma mata kaso 20.

Sai dai ya ce za a raba adadin da za a diba ne ga dukkan Kananan Hukumomin Jihar, inda ya ce kaso 70 cikin 100 na wadanda za a diba za su kasance cikin dakarun hukumar da aka dauka kwanakin baya, sai kuma ragowar 30 din da za su zama sabbin diba.

A bara ne dai Gwamnan na Kano ya amince da dibar dakaru 5,700 ga hukumar.

Babban Kwamandan hukumar ya shawarci dukkan masu neman gurbi a hukumar su tuntubi Kananan Hukumominsu na ainihi.