Hotuna: Yadda ‘yan arewa mazauna Ondo suka yi dandazon tarbar gwamna Akeredolu
Dubban ‘yan asalin arewacin Najeriya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ondo ne suka yi dafifi domin yiwa gwamnan jihar kana dan takarar gwamna a Zaben…
DagaAbbas Dalibi, a Akure
Sun, 27 Sep 2020 21:46:05 GMT+0100
Dubban ‘yan asalin arewacin Najeriya ‘yan jam’iyyar APC a jihar Ondo ne suka yi dafifi domin yiwa gwamnan jihar kana dan takarar gwamna a Zaben 10 ga watan Oktoba, Oluwarotimi Akeredolu mubayi’a.
Gwamna Akeredolu ya sami tarba daga kungiyar yan Arewa mazauna jihar ta shirya a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Alhaji Lawal Muhammad Shu’aibu a ranar Lahadi 27 ga watan Satumba a filin taro na Arcade da ke garin Akure Babban birnin jihar.
Gwmanan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu tare da Sarkin Hausawan Akure Alhaji Babangida Sadik a lokacin da ake masa addu’a a sa’ilin taron
Sashe na ‘yan Arewa mazauna jihar Ondo a lokacin da suke wa gwamna Akeredolu lale da zuwa taron da suka shirya
Wani sashe na mahalarta taron a lokacin da suke wa gwamnan sowa tare da daga hannun hudu alamar sai ya kara shekaru hudu a gadon mulkin jihar
Gwamnan jihar Ondo tare da wasu shugabannin yan Arewa mazauna jihar
Wani sashe na mahalarta taron dauke da hoton gwamnan
Shugaban kungiyar ‘yan Areawa mazauna jihar Ondo a lokacin taron
Wani sashe na mahalarta taron
Sashen mahalarta taron
Gwamnan a lokacin da yake zanta wa da Sarkin Hausawan Akure
Sashen mata mahalarta taron
Wata mace a lokacin da take jinjina ga gwamna Oluwarotimi na jihar Ondo