✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan ziyarar Sarkin Kano a Ilori

A cikin makon nan ne Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar aiki ta kwana uku a Jihar Kwara. Ga wasu…

A cikin makon nan ne Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya kai ziyarar aiki ta kwana uku a Jihar Kwara.

Ga wasu daga cikin kayatattun hotunan irin tabar da ya samu da ziyarar da ya kai garin Ilori:

Dubban jama’a a kan tituna suna murna yayin da mahaya dawakai ke masa rakiya.
Babu masaka tsinke a kan titi saboda yadda mutane suka fito tarbar Sarkin Kano a garin Ilori
Sarki Aminu Ado Bayero a kan keken dawakai, yana karbar gaisuwa daga masoya
Cincirindin mutane na rakiyar tawaga Sarki Aminu Ado Bayero a ziyarar da ya kai zuwa Ilori.
Taron jama’a biye da tawagar Sarki Aminu Ado Bayero a ziyarar da ya kai Ilori.
Dogarai sun rako Mai Martaba Sarki Aminu zai shiga mota
An dauko sarki a kan kekenshi zuwa fadar Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari
Keken dawakai na Sarkin Kano, dauke da tambarin ‘Magajin Dabo’ a jikinsa
Tun saukarsa a filin jirgi na Ilori Sarki Aminu ya tarar da cincirindon masu tabar shi.
Tawagar Sarkin Kano da ‘yan rakiya a ziyar da ya kai Ilori.