✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hukumar NEDC za ta gina makaranta a Yobe

Hukumar Bunkasa Arewa maso Gabas NEDC, za ta gina makaranta a garin Gashuwa da ke Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe a kokarinta na inganta…

Hukumar Bunkasa Arewa maso Gabas NEDC, za ta gina makaranta a garin Gashuwa da ke Karamar Hukumar Bade ta Jihar Yobe a kokarinta na inganta harkokin ilimi a yankunan da suka sha fama da rikicin Boko Haram.

Babban Manajan NEDC, Alhaji Mohammed G. Alkali da Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan su ne suka kaddamar da aikin gina makaranta ta farko.

A jawabin Babban Manajan Hukumar, ya ce Jihar Yobe ce ta farko da za ta fara amfana da irin wannan aiki na gina makarantar boko ta zamani.

A cewarsa da irin wannan ci gaba Jihar Yobe a yanzu ta kasance jihar da ke kan gaba wajen cika sharuddan da hukumar take bukata don amfana da irin ayyukan hukumar.

A kwanakin baya Gwamna Buni da hadin gwiwar Hukumar NEDC sun aza tubalin gina gidaje 500 a garin Damaturu wanda shi ne na farko a wannan yanki da Hukumar NEDC za ta aiwatar bayan kaddamar da gina hanyar Gujba zuwa Mutai.

Gwamna Buni wanda Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Yobe, Alhaji Abdullahi Yusuf Gashuwa ya wakilta da Sanata Ahmed Lawan Ibrahim wanda Sanata Yusuf A. Yusuf, Shugaban Kwamitin Ayyuka na Musamman a Majalisar Dattawa ya wakilta sun yi jinjina ga Hukumar NEDC bisa wannan kyakkyawan kudiri na habaka harkokin ilimi a yankin.