✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina cikin takaici kan irin abincin azumi da ake raba wa Kanawa — Gwamnan Kano

Abin da na gani a wannan ziyara ta ba-zata yana da takaici, duk kuwa da isasshen abinci da muka bai wa cibiyar.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaici matuƙa kan irin abincin da ya gani ana raba wa Kanawa a wannan wata na Ramadana.

Gwamnan ya ce ya ba da umarni a gudanar da bincike kan mutanen da gwamnatinsa ta bai wa kwangilar raba wa al’ummar jihar abincin.

Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan ya kai ziyarar ba-zata a Gidan Maza, ɗaya daga cikin cibiyoyin da aka ɗora wa alhakin raba abincin azumi da ke Karamar Hukumar Birni domin gane wa idanunsa abin da ke faruwa.

Gwamnan ya bayyana matuƙar ɓacin ransa dangane da ingancin abincin da ake bai wa jama’a yana mai cewa ba zai lamunci hakan ba.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta ranar Juma’a da maraice, an ga Abba Gida-Gida a cibiyar raba abincin inda ya ɗauki fanken da ake rabawa yana cewa “ku kalli wannan shirmen.”

Ya tambayi matan da ke soya fanken wanda ya ba su aikin inda suka bayyana cewa wani jami’in gwamnati ne.

Daga nan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tambaye su ko ana zuwa ana duba yadda suke gudanar da aikinsu. Matan sun bayyana cewa wasu jami’a suna zuwa.

Gwamnan ya umarce su da su inganta yadda suke soya fanken, yana mai cewa “kada na sake dawowa na tarar an yi abin da ba daidai ba.”

Daga bisani Gwamna Abba Kabir Yusuf ya wallafa saƙo a shafukansa na sada zumunta cewa ya bayar da umarni a gudanar da bincike kan yadda ake raba abincin na azumi.

“Da maraicen yau, na kai ziyara Gidan Maza, ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke rabon abincin azumin Ramadan a ƙaramar hukumar Birni.

“Abin da na gani a wannan ziyara ta ba-zata yana da takaici, duk kuwa da isasshen abinci da muka bai wa cibiyar.

“Na yi umarni a gudanar da cikakken bincike, kuma na bayar da umarni a yi gaggawar sauya tsarin wannan shiri,” in ji gwamnan Kano.

Aminiya ta ruwaito cewa an yi ta cece-kuce kan shirin ciyarwar watan Ramadan da ake gudanarwa a jihar.

Lamarin na zuwa ne tun bayan da Gwamnatin Kano ta ce ta ware Naira biliyan 6 domin gudanar da wannan aiki da wasu ke ganin akwai kura-kurai a ciki la’akari da maƙudan kuɗin da ake ikirarin kashewa.