INEC za ta tsawaita wa’adin yin rajistar katin zabe —Farfesa Yakubu | Aminiya

INEC za ta tsawaita wa’adin yin rajistar katin zabe —Farfesa Yakubu

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood
    Ishaq Isma’il Musa da Abbas Jimoh

Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta ce za ta kara wa’adin yin rajistar katin zabe a fadin kasar baki daya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Asabar a wurin taron tunatar da matasa muhimmancin kuri’unsu a zabe.

A yayin taron wanda aka gudanar a tsohon filin faretin dakarun soji da ke Abuja, wakilinmu ya ruwaito cewa, Farfesa Yakubu ya yi shiru kan tsawon lokacin da INEC za ta kara na wa’adin yin rajistar.

“Lallai wannan ya nuna Matasa suna son sanin lokacin da za a rufe rajistar katin zabe.

“Saboda haka ina so in tabbatar muku a madadin Hukumar INEC cewa ba za a rufe rajistar ba a ranar 30 ga watan Yuni ba domin kuwa, matukar akwai mutanen da ke son yin rajista, za mu ci gaba da yi musu rajista.

“A cikin kwanaki biyar da suka gabata, mun yi wa ‘yan Najeriya sama da 14000 rajista a wannan haraba kadai, sannan muna da na’urorin yin rajistar katin zabe kusan 50,” inji Yakubu.

Farfesa Yakubu ya jaddada abubuwa masu muhimmanci yayin bayanin nasa da suka hada da yin rajistar da kuma karbar katin zaben.

Kazalika ya yi bayanin kan cewa mutane su guji sayar da kuri’arsu, duk wanda ya yi kuri’a ya tabbatar da cewa ya yi zabe a ranar zabe.

Shugaban INEC din ya nuna cewa zaben 2023 zai zama mai tsafta, wanda babu cuta babu cutarwa cikinsa.

Daidaikun mutane da kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam dai sun yi ta kiraye-kirayen a kara wa’adin yin rajistar, saboda wadanda ba su yi ba da wadanda ta su ta bata da wadanda ke son a sauya musu wurin yin zaben da dai sauransu.