✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran ta zartas da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga biyu

Tun bayan barkewar zanga-zanga a watan Satumbar bara, an yanke wa mutum fiye da hudu hukuncin kisa a Iran.

Rahotanni na cewa Gwamnatin Iran ta zartas da hukuncin kisa kan wasu masu zanga-zanga biyu a ranar Asabar.

Hukuncin dai na zuwa ne bayan samunsu da gwamnatin ta ce ta yi da laifin kashe wani jami’in tsaro a lokacin zanga-zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini.

Wadanda aka kashen sun hada da Mohammed Mahdi Karami da Seyyed Mohammad Hosseini.

Tun dai bayan barkewar zanga-zangar adawa kan mutuwar Mahsa Amini a watan Satumbar bara, an yanke wa mutum fiye da hudu hukuncin kisa ta hanyar rataya a kasar ta Iran, lamarin da ya janyo wa kasar suka daga manyan kasashen duniya.

Ko a nan birnin Bonn da Yammacin ranar Asabar, daruruwan al’umma ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da mahukuntan na Iran ke dauka a kan masu boren.

A cewar dan Majalisar Dokokin Jamus Helge Limburg, Jamus da Amurka gami da Kungiyar Tarayyar Turai ba za su zuba ido a kan hukuncin kisa da mahukuntan Tehran ke aiwatarwa a kan fararen hula ba.