✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Isra’ila ta kaddamar da gasar Baibul a Najeriya

Kasar Isra’ila ta fara rajistar masu son shiga gasar Baibul ta Kasa Karo na Uku a Najeriya. Jami’a mai kula da Hukumar Raya Kasashe ta…

Kasar Isra’ila ta fara rajistar masu son shiga gasar Baibul ta Kasa Karo na Uku a Najeriya.

Jami’a mai kula da Hukumar Raya Kasashe ta Isra’ila (MASHAV) a ofishin jakadancin kasar da ke Najeriya, Chikadibia Kene-meenu, ta sanar da haka ranar Laraba a Abuja.

“Wata sabuwar dama ta bude ta yin rajista don shiga gasar daga yanzu har zuwa ranar 12 ga watan Agusta.

“Ranar 13 ga watan Agusta kuma za a yi gwaji ta intanet a fadin Najeriya.

A cikin kasa da sa’a guda bayan kammala gwajin kuma za a tura wa wadanda suka yi shi rariyar likau (wato link) ta jarrabawar.

“Za a zabi mutum biyu da suka fi yawan maki daga ko wacce jiha don su fafata a mataki na gaba”, inji ta.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato ta tana cewa an dauki nauyin ziyarar wadanda suka yi nasara a gasar baya zuwa Isra’ila, inda suka ziyarci wurare masu tsarki sannan suka bakunci Gasar Baibul ta Birnin Kudus.

A kan shirya gasar ne dai ta intanet duk shekara yayin da ake karawa ta karshe a Abuja.