✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta kai hari masallacin birnin Kudus, ta raunata masallata 158

Sun kai hari ne da sanyin safiyar Juma’a, lokacin sallar Asuba

’Yan sandan Isra’ila sun mamaye masallacin birnin Kudus, inda suka raunata Falasdinawa 158 da ke ibada a masallacin, sannan suka tsare wasu da dama.

Rahotanni sun ce ’yan sandan Isra’ilan sun kai harin ne gabanin sallar Asuba ta ranar Juma’a lokacin da dubban mutanen suka taru a masallacin don yin Sallah.

Wasu faya-fayan bidiyo da suka karade kafafen sada zumunta sun nuna Falasdinawa na jefa duwatsu a kan ’yan sandan da ke fesa musu barkonon tsohuwa da gurneti.

Wasu kuma sun nuna yadda masallatan ke kakkange junansu a cikin masallacin daga tukukin barkonon tsohuwar.

Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent da ke kasar dai ta ce jami’an agaji sun kwashe mutanen da suka ji rauni zuwa asibitoci, cikinsu har da wani mai gadin masallacin da aka harba da harsashin roba a ido.

Kazalika, kungiyar ta ce Isra’ila ta kuma hana motocin daukar marasa lafiya zuwa cikin masallacin, a daidai lokacin da aka yi wa masallata da dama kofar rago a cikinsa.

’Yan Sandan na Isra’ila sun ce sun kama akalla Falasdinawa 300, ko da yake majiyoyin Falasdinawan sun ce mutanen da aka kama sun kai 400.

Masallacin birnin Kudus dai shi ne na uku mafi tsarki a masallatan da Musulmai ke tunkaho da su a duniya, inda su ma Yahudawan ke ganinsa a matsayin wata alama ta addinsu.

Ko a watan azumin Ramadan na bara ma sai da Isra’ila ta shafe kusan kwana 11 tana mamayar masallacin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 260 da Yahudawa 13 sannan aka lalata sassan masallacin da dama.

Azumin bana dai ya hade da lokacin da Yahudawa ke bikin addininsu wato Passover, yayin da su kuma Kiristoci ke bukukuwan Easter, lamarin da ya sa dubban mutane ke ziyartar birnin na Kudus.