✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’a ta bude cibiyar bincike kan kansar bakin mahaifa a Kano

Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano (YUMSUK) ta kaddamar da cibiyar bincike don gano kansar bakin mahaifa. Da yake kaddamar da cibiyar ranar Laraba,…

Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano (YUMSUK) ta kaddamar da cibiyar bincike don gano kansar bakin mahaifa.

Da yake kaddamar da cibiyar ranar Laraba, Shugaban Jami’ar, Farfesa Mukhtar Atiku-Kurawa, ya ce an gina ta a harabar jami’ar ne domin bincike a kan larurar wadda ke kara yaduwa a tsakanin mata.

Ya kuma ce wannan dakin gwajin shi ne irinsa na farko a arewacin Najeriya, kuma zai taimaka wajen ganowa da kuma yi wa matan da ke dauke da larurar magani, musamman wadanda suka fito daga jihohin Jigawa, da Katsina, da kuma Kano.

Kazalika Farfesa Kurawa ya ce ginin dakin gwajin ya samu ne da tallafin Asusun Tallafa wa Makarantun Gaba da Sakandare wato TETFUND.

Haka kuma an jibge na’u’rorin zamani domin tabbatar da dorewar aiki mai inganci da  kuma binciken cutar, a cewarsa.

Farfesa Kurawa ya kuma ce ko da yake jami’ar sabuwa ce kuma ta jiha, ta cimma nasarori da dama.