✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’o’in Najeriya da suka yi zarra a duniya

Wadanda suka ciri tuta su ne Jami'o'in da suka fi yin zarra su ne da Jami'ar Ibadan, Jami'ar Legas, Jami'ar Covenant, Jami'ar Bayero, da Jami'ar…

Shugaban Kwamitin Tantance Darajar Jami’o’in Najeriya (NURAC), Farfesa Peter Okebukola ya ce, akalla jami’o’in Najeriya 12 sun samu cigaban da ya kai sun sha yabo a wajen babban taron ilimi da aka kammala kwanan nan a birnin New York na kasar Amurka.

Okebukola ya bayyana hakan ga mana labarai ne jim kadan bayan da ya dawo Abuja daga wajen taron.

A cewarsa, jerin jami’o’in da suka fi yin zarra su ne da Jami’ar Ibadan da Jami’ar Legas da Jami’ar Covenant da Jami’ar Bayero Kano sannan Jami’ar Tarayya da ke Akure.

Sauran su ne, Jami’ar Ilorin da Jami’ar Najeriya, Nsukka da Jami’ar Obafemi Awolowo da Jami’ar Harkokin Noma da ke Abeokuta da Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, sai kuma Jami’ar Nnamdi Azikiwe.

Jami’in ya ce a halin da ake ciki Jami’ar Legas ita ce kan mataki na 478 a duniya sannan ta daya a Najeriya.

Ya ce Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed ne ya kafa NURAC da nufin sanya wa jami’o’in Najeriya kaimi domin bunkasa su da kuma ba su damar gogayya da takwarorinsu a sassan duniya.

Ya kara da cewa, a tsakanin watanni 12 da suka gabata, NURAC ya yi aiki babu kama hannu yaro domin sauke nauyin da aka dora masa.

A yanzu dai jami’o’i biyar da suka yi wa takwarorinsu fintinkau a fadin duniya 2023 su ne, Oxford da Harvard da Cambridge da Stanford, sai kuma MIT.