✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin ’yan Super Eagles 23 da za su buga wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya

Za a buga Gasar Kofin Duniya a Amurka da Canada da Mexico a 2026.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta fitar da sunayen ’yan wasa 23 da Jose Santos Peseiro ya gayyata, domin buga wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya.

Super Eagles, wadda za ta buga Gasar Kofin Afirka a Ivory Coast a 2024, za ta fara wasannin neman shiga Gasar Kofin Duniya da Lesotho, sannan ta je Zimbabwe.

Za a buga Gasar Kofin Duniya a Amurka da Canada da Mexico a 2026, inda Najeriya za ta fara wasa da Lesotho ranar Alhamis a Uyo.

Daga nan za ta je Rwanda, domin fafatawa da Zimbabwe ranar 19 ga watan Nuwamba a filin wasa na Huye da ke Butare.

Zimbabwe tana buga wasanninta a Rwanda, kasancewar ba ta da wani filin a zo a gani da ya cika ka’idar da Hukumar Kwallon Kafar Duniya FIFA ke bukata.

’Yan wasan tawagar Super Eagles:

Masu tsaron raga: Francis Uzoho (Omonia FC, Cyprus); Olorunleke Ojo (Enyimba FC); Maduka Okoye (Udinese Calcio, Italy).

Masu tsaron baya: Olaoluwa Aina (Nottingham Forest, England); Chidozie Awaziem (Boavista FC, Portugal); Bright Osayi-Samuel (Fenerbahce FC, Turkey); Bruno Onyemaechi (Boavista FC, Portugal); Kenneth Omeruo (Kasimpasa FC, Turkey); Oluwasemilogo Ajayi (West Bromwich Albion, England); Calvin Bassey (Fulham FC, England); Jamilu Collins (Cardiff FC, Wales).

Masu buga tsakiya: Raphael Onyedika (Club Brugge, Belgium); Joe Ayodele-Aribo (Southampton FC, England); Frank Onyeka (Brentford FC, England); Alex Iwobi (Fulham FC, England).

Masu buga gaba: Kelechi Iheanacho (Leicester City, England); Sadiq Umar (Real Sociedad, Spain); Moses Simon (FC Nantes, France); Ademola Lookman (Atalanta FC, Italy); Nathan Tella (Bayer Leverkusen, Germany); Taiwo Awoniyi (Nottingham Forest, England); Terem Moffi (OGC Nice, France); Victor Boniface (Bayer Leverkusen, Germany).