✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibge jami’an tsaro awa 24 a hanyoyi zai magance satar mutane —Matasa

Matasan Najeriya sun shawarci Gwamnatin Tarayya ta jibge jami’an tsaro ba dare, ba rana a kan dukkannin manyan hanyoyi domin kawar da ayyukan ’yan fashi…

Matasan Najeriya sun shawarci Gwamnatin Tarayya ta jibge jami’an tsaro ba dare, ba rana a kan dukkannin manyan hanyoyi domin kawar da ayyukan ’yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Matasan daga kabilu da addinai da sana’o’i da ra’ayoyin siyasa mabambanta sun yi kiran ne a taron da suka gudanar kan matsalolin da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya ranar Litinin a Abuja.

Sun kuma ba da shawarar a share duk shuke-shuken da ke gefen hanyoyin na tsawon kilomita daya domin tabbatar da tsaro.

Kungiyar matasan mai suna Unity in Diversity Forum ta koka kan karuwar miyagun laifuka a Najeriya.

Ta kuma bukaci a ba wa sarakunan gargajiya matsayi a kudin tsarin mulkin kasa domin takaita aikata laifuka a cikin al’ummomi.

Da take kokawa game da tabarbarewar al’amuran tsaro, tattalin arziki, ilimi da abubuwan more rayuwa a kasar, kungiyar ta bukaci a ingata tare da samar da isasshen ilimi ga dukkanin ’yan Najeriya.

Sannan ta jaddada muhimmanci amfani da kafofi irin Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) da sauran masu fada a ji wajen ganin tabbatuwar hakan.

“Daidaiton ilimi (inganta ilimin ’ya’ya mata) ne ya kamata a fara ba wa muhimmanci kafin batun samar da ilimin da kuma inganta shi.

“Ba komai ya kawo matsananciyar fatarar da ake fama da ita a Arewacin Najeriya ba face wariya da tauye hakkin mata wadanda su ne akasarin al’ummar yankin”, inji sanarwar bayan taron.

Matasan da suka koka kan rashin kyakkyawan shugabanci a matakin Kananna Hukumomi sun bukaci a gyara tsarin zabe a matakin domin samar da managarcin shugabanci ga al’umma.