✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto matar da ’yan uwanta suka kulle watanni 5 a daki

Ana zargin yayyenta da kulle ta a daki bayan sun zarge ta da yin 'cikin shege'

Hukumar tsaro ta NSCDC a jihar Gombe ta ceto wata mata mai kimanin shekara 35 wacce ’yan uwanta suka kulle a wani daki tsawon wata biyar.

An dai ceto matar mai suna Saratu Ayuba da ke zaune a unguwar Bolari da ke garin Gombe ne a karshen makon jiya bayan samun bayanai daga makwabtanta da suka yi zargin ana azabtar da ita.

Ana zargin wasu yayyen Saratun ne suka kulle ta a wani daki na tsawon wannan lokacin bayan sun zarge ta da yin cikin shege da kuma haifewa.

Shaidu sun ce an kulle ta ne a dakin tare da jaririyar da ta haifa mai kimanin wata biyu da haihuwa a wani kuntataccen daki.

Saratu, wacce ke cikin wani yanayi mara kyan gani lokacin da aka kubutar da ita ba tare da ko suturar kirki ba ta ce tsuran ruwan shayi da burodi kawai ake ba ta a matsayin abinci tsawon wannan lokacin.

Hakan, a cewarta ya yi mummunan tasiri ta yadda ba ta iya samar da wadataccen ruwan nono domin shayar da jaririyarta.

Sai dai ta ce cikin da ake zarginta da shi ba na shege ba ne, hasali ma na tsohon mijinta wanda ya yi mata domin ya tilasta wa ’yan uwan nata su kyale ta ta koma gidansa, tana mai cewa ya yi mata saki biyu ne tun da farko cikin kuskure.

Ta kara da cewa ta haifi ’ya’ya biyu a aurenta na farko; Alkasim mai shekaru 10 da kuma Fatima shekara takwas.

Su kuwa a nasu bangaren, yayan Saratu mai suna Muhammad Tajuddin ya ce sun kulle ta ne bayan likitoci sun yi bincike tare da gano tana da tabin hankali.