✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jiragen soji sun kashe ’yan ta’adda sama da 100 a Borno

Jiragen sojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun kashe ’yan ta'addan kungiyar ISWAP fiye da 100 a yankin marte da ke Jihar Borno

Jiragen sojin Najeriya daga rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe ’yan ta’addan kungiyar ISWAP fiye da 100 a yankin marte da ke Jihar Borno.

Wata majiyar soji ta shaida wa Zagazola Makama cewa an kai harin ta sama ne a tsakiyar wannan wata na Oktoba 2023 a lokacin da ’yan ta’addan ke ganawa a dajin Bukar Mairam a Karamar Hukumar Marte.

Ya ce “Dandalin ISR ya hango wani gagarumin motsi na ’yan tada kayar baya na tafiya zuwa wani wuri da ake zargin cibiyarsu ce, aka shammace su da ruwan bama-bomai ta sama aka yi kaca-kaca da su da abubuwan hawansu hade da makaman da ke tattatare da su.

Majiyar ta bayyana “’yan ta’addar sun shirya taro a yankin ne domin shirya kai hare-hare da daddare a kan wuraren da sojojin suke,” in ji majiyar.

Idan ba a manta ba, a ’yan kwanakin nan, ruwan bama-bamai da sojojin saman Najeriya suka yi da kuma aikin share fage da sojojin kasa suka yi, sun hallaka dimbin ’yan bindiga da ’yan ta’addar ISWAP a yankunan Arewa maso Gabas.