✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jirgin fasinja mai tarago 21 yi hatsari a Indiya

Akalla mutum hudu ne suka rasu wasu da sama suka samu raunuka bayan wani jirgin kasan fasinja ya yi hatsari a Jihar Bihar ta kasar…

Akalla mutum hudu ne suka rasu wasu da sama suka samu raunuka bayan wani jirgin kasan fasinja ya yi hatsari a Jihar Bihar ta kasar Indiya.

Rahotanni sun ce jirgin kasan dauke da fasinjoji zuwa birnin Delhi daga tashar Anand Vihar, taragansa 21 ne suka sauka daga layin dogo a daren Laraba.

A safiyar Alhamis wani babban jami’in sufurin jiragen kasa, Tarun Prakash, ya sanar cewa “ana ci gaba da aikin ceto amma mutum hudu sun mutu, wasu da dama sun jikkata bayan hatsarin jirgin kasan.

Ministan sufurin jiragen kasa, Ashwini Vaishnaw ya jajanta wa wadanda hatsarin ya shafa, yana mai cewa an sauya wa fasinjojin jirgi domin karasa tafiyar tasu, amma mai yi magana kan mamatan ba.

Sai dai rahotanni sun ce an garazaya da wadanda suka samu rauni asibiti domin ba su kulawa.

Indiya na daga kasashe da mafiya amfani da jiragen kasa, kuman an sha samun haddura, mafi munin shi ne wanda mutum 800 suka rasu a shekrar 1981 sakamakon faduwar wani jirgin kasa a cikin kogi daga saman gadar jihar Bihar.A watan Yuni mutum 300 sun mutu a sakamakon taho-mu-gaman jiragen kasa a Jihar Odisha. sannan a Agusta wasu tara suka rasu a gobarar da ta tashi a taragon wani jirgin fasinja a yayin da fasinjoji ke hada shayi.