✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jonathan ya yi watsi da fom din takarar APC da aka saya mishi

Tsohon shugaban kasar ya yi godiya ga masu son ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya nesanta kansa da fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da wata kungiya ta saya mishi.

A wata sanarwa da ofishin yada labaran tsohohon shugaban kasar ya fitar sa’o’i kadan bayan kungiyar ta sayi fom din a kan Naira miliyan 100, Jonathan ya bayyana kyamarsa ga matakin, yana mai jaddada cewa shi ba dan jam’iyyar APC ba ne.

“Saboda haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da abin da kungiyar ta aikata, domin ba da sanin Dokta Goodluck Jonathan ko izininsa ta yi ba,” inji sanarwar.

A ranar Litinin da yamma ne dai wata bakuwar kungiya mai suna ‘Kungiyar Fulani’ ta saya wa tsohon shugaban kasar fom din, duk da cewa bai taba bayyana cewa ya koma jam’iyyar APC ba.

Jim kadan bayan nan ne ofishinsa na yada labarai ya sanar cewa, “Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya samu labarin wata kungiya mai suna “Fulani Group” ta sayi fom din takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da sunansa.

“Muna sanar da jama’a, musamman al’ummar Najeriya cewa Dokta Goodluck Jonathan ba shi da masaniya ko wata alaka da sayen fom din da aka yi da sunansa, hasali ma ba shi da kowace irin alaka da kungiyar.

“A sani cewa a halin yanzu Dokta Jonathan ba dan jam’iyya APC ba ne, don haka ba za ta taba sabuwa ba ya yi na’am da irin wannan tayi daga masu wannan yunkuri.”

Duk da haka sanarwar ta bayyana godiyar Jonathan ga ’yan Najeriya da ke ta kiraye-kirayen ya fito takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 da ke kara matsowa.

Amma ofishin ya ce, “Muna kara jaddada cewa a halin yanzu ba shi da aniyar karbar wannan tayin da ake yi mishi, duk da cewa akwai masu ganin cewa fitowar tasa ita ce kishin kasa.

Wasu majiyoyi masu tushe sun shaida wa Aminiya cewa wasu gwamnoni biyu a jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya ne kan gaba a yunkurin da ganin Jonathan ya gaji Buhari a 2023.

Daya daga cikin gwamnonin, wanda a baya-bayan nan suke yi uwa suke makarbiya a APC, ya fito ne daga yankin Arewa ta Gabas, dayan kuma daga Arewa ta Yamma.

Majiyar ta ce kowanne daga cikin gwamnonin biyu na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari na.