✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Juyin mulki: Sojoji sun sassauta dokar hana fita a Mali

Bayan juyin mulkin da sojojin Mali suka yi yanzu sun sassauta dokar hana fita

Kwamitin da aka kaddamar bayan juyin mulkin kasar Mali ya sanar da sassauta dokar hana fita a ranar Juma’a.

Kwamitin Kasa don Ceton Jama’a na ‘National Committee for the Salvation of the People (CNSP),’ na sabuwar gwamnatin da manyan sojojin kasar da suka kafa bayan juyin mulkin ya sanar da hakan.

Kakakinta, Ismael Wague ya shaida wa mujallar kasar ta Journal du Mali cewa: “CNSP na sanar da ’yan kasar Mali cewa, an sassauta dokar hana fita da aka kakaba bayan juyin mulki.

”Daga yanzu dokar za ta fara ne daga karfe 12:00 na tsakiyar dare zuwa karfe 5:00 na asuba,’’ inji Wague.

An dai sanya dokar hana fitar ne ranar Laraba 12 ga watan Agusta 2020 daga karfe 9:00 na dare zuwa karfe 5:00 na asuba.

An kuma yi juyin mulkin ne a ranar Talata wand aka fara daga barikin sojoji na Kati da ke makwabtaka da Bamako babban birnin kasar.

Masu juyin mulkin sun tsare Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Firayi Minista Boubou Cisse da wasu manyan jami’an gwamnatin kasar.

Daga bisani Shugaba Keita ya sanar da yin murabus dinsa daga mulki tare da rushe jami’an fadarsa.

Sojojin da suka yi juyin mulkin, sannan suka kaddamar da kwamitin riko na CNSP sun rufe duk iyakokin kasar saboda dokar hana fita.