✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu sa kafar wando da masu ambato juyin mulki —Sojoji

Rayuwa ta yi tsada a Najeriya, lamarin da ya sanya wasu fara kiranye-kiranye da sojoji su yi juyin mulki.

Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin kasar nan.

Najeriya dai na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abin da ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar nan.

Wasu daga cikin ’yan kasar sun jima suna kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu tare da karbe iko kamar yadda aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Sai dai Daraktan Tsaro na Sojin Najeriya, Janar Christoper Musa, ya ce masu wannan kiraye-kiraye ba sa nufin kasar da alkahairi.

Kazalika, dakarun sojin Najeriya za su sa kafar wando daya da masu wannan kiranye-kiranye.

Ya ce abin da sojoji za su yi a yanzu shi ne kawai duba hanyoyin samar da sauki da kuma ciyar da kasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba.

Da yake amincewa da halin matsi da ’yan Najeriya ke ciki, Janar Musa, ya ce babu inda juyin mulki ke zama alkahairi a duniya don haka ba za su yi wa Najeriya fatan ci bayan da yake biyo bayan juyin mulki ba.

Ya bukaci ’yan Najeriya da su kara hakuri da halin da kasar ke ciki.

Har wa yau, ya bukaci su kasance masu juriya don cin moriyar tsare-tsaren da gwamnati ke bijirowa da su a nan gaba.

’Yan Najeriya dai na ci gaba da nuna bacin ransu kan yadda kayan abinci ke tashin gwauron zabi.

Kazalika, sun koka kan yadda rayuwa ta yi tsada biyo bayan janye tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya yi a watan Mayun 2023.