✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kalubalen da ke gaban sababbin hafsoshin tsaro

Manyan kalubalen da harkar tsaron Najeriya ke fuskanta shi ne rashin tattara sahihan bayanan sirri.

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya sallami manyan hafsosin tsaron Najeriya tare da maye gurbinsu da wasu sababbi.

Shugaban ya kuma daga likafar Nuhu Ribadu zuwa matsayin Mai ba shi Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa (NSA).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar a daren na Litinin.

Wadanda aka sallama su ne Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor da Babban Hafsan Sojojin Kasa, Farouk Yahaya da na Ruwa, Awwal Gambo da na Sama, Isiaka Amao, sai kuma Babban Sufeton ’Yan sanda, Usman Alkali Baba.

Sabbin wadanda aka nada su ne Manjo Janar C.G Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaro da Manjo Janar T. A Lagbaja a matsayin Shugaban Sojojin Kasa, sai Riya Admiral E. A Ogalla a matsayin Shugaban Sojojin Ruwa, sai Iya Bayis Mashal H.B Abubakar a matsayin Babban Hafsan Sojojin Sama.

Kazalika, Shugaba Tinubu ya sallami Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya) daga matsayin mai ba da shawara kan tsaron kasa, inda ya maye gurbinsa da Nuhu Ribadu. Idan ba a manta ba, matsala tsaro na cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fama da su a yanzu.

Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaji matsalar Boko Haram da ta fi kamari a yankin Arewa maso Gabas, da masu fasa bututun mai a yankin Kudu maso Kudu.

Sai dai tsohon Shugaban ya yi kokarin rage rikicin Boko Haram da kaso mafi girma, amma shi ma ya gadar da wasu rikice-rikicen da suka yi kamari.

Daga cikin matsalolin da Shugaba Tinubu ya gada akwai matsalar ’yan bindiga da ta fi kamari a yankin Arewa maso Yamma, wanda ko a zamansa da gwamnoni na farko, sai ya zauna na daban da gwamnonin yankin kan matsalar da ’yan IPOB da sauransu.

Wannan ya sa masana suke ganin zai fi kyau idan Shugaba Tinubu ya fara magance rashin tsaro, wadda ta kunshi ta’asar ’yan bindiga da garkuwa da mutane da ta’addanci da satar mai da yunkurin ballewa daga kasa da fadace-fadacen ’yan kungiyoyin asiri da rikicin manoma da makiyaya da rikicin kabilanci da damfarar intanet da sauransu.

Kowace daga cikin shiyyoyin siyasa shida na kasar nan a yanzu tana fama da irin tata matsalar tsaron duk da tsoma sojoji a cikin lamarin a tsawon shekaru.

Misali wasu jihohi a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya suna fama da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga, yayin da Neja-Delta ke fama da barayin mai.

Sannan bincike ya nuna har yanzu ’yan ta’addan Boko Haram tafka barna a Arewa maso Gabas.

Har yanzu dai Najeriya ta fi dogaro da man fetur, wanda hakan ya sa kalubalen tsaro a yankin da aka fi samar da man zai iya zama babbar barazana ga kasar.

Sannan ’yan fafutikar awaren Biyafara, wato IPOB sun dade suna cin karensu ba babbaka. Aminiya ta ruwaito yadda ’yan Boko Haram da ’yan fashin daji da masu rajin kafa kasar Biyafara (IPOB) da wasu tsirarun mutane suka kasha kimamin sojoji da ’yan sanda 965 a bakin aikinsu a cikin shekara biyu.

Aminiya ta bi diddigi tare da binciko yadda aka kashe wadannan jami’ai a tsakanin watan Janairun shekarar 2021 zuwa watan Afrilun 2023, inda sakamakon binciken ya gano cewa jami’an tsaron Najeriya sun hadu da dimbin asarar rayuka sakamakon kisansu da wasu ba suka yi.

A binciken da ta yi ta hanyar tattara rahotannin jaridu dabandaban a kan kisan jami’an tsaro da aka bayar da rahoto, ta gano cewa ’yan sanda 581 da sojoji 384 ne aka kashe a bakin aiki a tsakanin wannan lokaci.

Wannan ke nan bayan daruruwan mutane da ’yan ta’addan nan suka kashe. Wanda hakan ya sa da dama ’yan Najeriya suka sa ido don ganin rawar da sababbin hafsoshin tsaron za su taka.

Yadda za su samu saukin aiki —Masani

Wani masani a kan harkokin tsaro Dokta Kabir Adamu da BBC ta tattauna da shi ya ce rahoton wani binciken da suka gudanar kuma suka mika wa Shugaban Kasa ya nuna cewa, daya daga cikin manyan kalubalen da harkar tsaron Najeriya ke fuskanta shi ne rashin tattara sahihan bayanan sirri, da tantance su, da kuma aiki da su yadda ya kamata.

Ya kara da cewa kowane bangare a cikin bangarorin tsaron kasar 27 yana fama da wannan matsalar, don haka, akwai bukatar mai bai wa Shugaban Kasa shawara a harkar tsaro ya bi diddigin wannan batu kuma ya sanya ido don tabbatar da samun mafita.