✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karamin yaro ya kashe ’yar aikin gida a Jihar Abiya

Wani yaro (an sakaya sunansa), dan shekara shida da haihuwa ya bindige wata ’yar aikin gida da ke aiki gida a gidansu a garin Aba,…

Wani yaro (an sakaya sunansa), dan shekara shida da haihuwa ya bindige wata ’yar aikin gida da ke aiki gida a gidansu a garin Aba, Jihar Abiya.
Wata majiya da ke kusa da iyalin da abin ya faru, sun shaida mana cewa yaron dan shekara shida da haihuwa ya shiga dakin babansa ne, ya ga bindiga, say a yi zaton irin tasu ce ta wasa. Sai ya dauko ya nufi waje, ya ga ’yar aikinsu tana aiki. Kamar wasa sai ya nuna ta, ya ce: “Sai fa in kashe ki…” Ashe bindigar a dure take da harsasai, kamar wasa yaron ya ja kunamar bindigar; ta kuma tashi. Sanadin haka yarinyar ta bakunci lahira.”
Aminiya ta tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Abiya, ASP Ogbonnaya Nta, domin jin gaskiyar labarin. Ya kuma gaskata faruwar hakan, inda ya ce yanzu haka ma “an mayar da batun gaban babban ofishin ’yan sandan jihar, sashen da ke binciken masu aikata miyagun laifuka.
Wasu mazauna jihar da aka ji ta bakinsu, sun dora alhakin lamarin a kan sakacin iyaye da kuma rashin rika adana makamai irin wadannan da kyau, domin guje wa yara.