✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin kudin mai da wuta: Buhari ya bukaci tattaunawa da ’yan kwadago

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Kwadago, Dakta Chris Ngige, ya tattauna da kungiyoyin ’yan kwadago don yi musu bayanin hakikanin halin da tattalin…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministan Kwadago, Dakta Chris Ngige, ya tattauna da kungiyoyin ’yan kwadago don yi musu bayanin hakikanin halin da tattalin arzikin kasa ke ciki.

Ana sa ran tattaunawar ne domin ganin an kaurace wa yiwuwar tsunduma yajin aikin ’yan kwadagon, a daidai lokacin da ake kokawa kan karin farashin kudin wutar lantarki da na man fetur.

Minista Ngige ne ya sanar da hakan a Abuja ranar Juma’a lokacin da yake wa ’yan jaridan fadar gwamnati jawabi bayan tattaunawarsa da Shugaba Buhari.

Ya ce an tsara tattaunawar za ta gudana ne ranar Asabar, 13 ga watan Satumbar 2020.

Ya kuma ce suna sa ran tattaunawar za ta ba kungiyoyin damar fahimtar yadda samun kudaden gwamnatin yake wanda ya tilasta mata karin kudaden.

Ya ce, “Shugaban kasa ya umarce mu da mu tattauna da su da kuma dukkan hukumomin gwamnati da ke da jibi da kudade domin nuna musu hakikanin halin da ake ciki.

“Yayin tattaunawar, za mu baje komai a faifai dangane da kudaden shiga na gwamnati da kuma kowanne irin kalubalen da ake fuskanta.

“Hakika duk abin da su ma suke tunani ko wata matsaya da za su dauka tana da muhimmanci ga ’yan Najeriya, musamman ma ma’aikata, saboda haka su ma za su fadi albarkacin bakinsu”, inji shi.

Ngige ya ce gwamnati ta kara kudaden ne da amincewar hukumomin da ke kula da sassan da aka yi karin la’akari da kalubalen da suke fuskanta.

Akan batun yiwuwar tsunduma yajin aikin ma’aikatan jami’o’i kuwa, ministan ya ce gwamnati na sane da su kuma tuni ma ta aike musu da goron gayyata domin tattaunawa.

Ya ce, “Mun gayyaci kungiyoyin NASU, SSANU da NAAT domin duba kalubalen tsarin biyan albashi na IPPIS. Suna ikirarin tsarin na cirar musu kudi na babu gaira ba dalili.

“Kazalika suna korafin cewa tsarin IPPIS ya cire su daga cin gajiyar duk wasu kudaden alawus-alawus da ma’aikatan jami’a ke amfana da su kamar na dawainiya, hatsari, tafiye-tafiye da na ilimin ’ya’yansu”, inji Ngige.