Karin mutum 395 daga cikin ’yan Najeriya da suka makale a kasar Saudiyya sun sauka a Abuja.
Mutnen sun iso ne a ranar Talata cikin jirgin kamfanin Saudi Air a Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe da.
- Hana ’yan bindiga sakat nake so ku yi —Buhari ga Hafsoshin Tsaro
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
- An kwaso ’yan Najeriya 255 da suka makale a Saudiyya
Sawu na biyu ke nan da aka kwaso na ’yan Najeriya da suka makale a kasar. Kawo yanzu, ’yan Najeriya 650 ne aka dawo da su daga Kasa Mai Tsarki.
Hukumar Kula da ’Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ta ce kafin karshen mako jirgi na uku zai kwaso karin wasu daga Saudiyya.
Hukumar ta ce za a killace mutanen da aka kwaso a sansanin alhazai na Abuja bisa dokar kariyar cutar COVID-19 kafin daga baya su koma ga iyalansu.