✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kasar Argentina ta halasta zubar da ciki

Hakan dai ya kawo cikas matuka ga dimbin tasirin da Darikar Cocin Katolika take da shi a yankin

Majalisar Dokokin Argentina ta amince da dokar halasta zubar da ciki a kasar, wanda hakan ya mayar da ita kasa ta hudu a yankin Latin Amurka da ta halasta shi.

38 daga cikin ’yan majalisar ne suka amince da kudurin, yayin da 29 suka nuna rashin amincewa da shi, a kasar da a baya ta haramta zubar da duk cikin da ya haura makonni 14.

Hakan dai ya kawo cikas matuka ga dimbin tasirin da Darikar Cocin Katolika take da shi a yankin wacce ke adawa da tsarin zubar da cikin.

Dubban mutane ne dai suka yi cincirindo a kofar majalisar suna rera wakokin neman a halasta dokar, a tsawon sa’o’i 12 da aka kwashe ana tafka muhawara a kan kudurin dokar.

Wata budurwa ’yar kasar mai kimanin shekaru 25, Viviana Rios Alvarado ta ce, “Gaskiya na yi matukar farin ciki da wannan ci gaban.

“Mun fuskanci abubuwa da dama mu da masoyan mu tsawon lokaci. Amma yau an kawo karshen lamarin. Wannan abin jin dadi ne matuka,” inji ta.

A wani sako da ya wallafa shafinsa na Twitter, Shugaban kasar ta Argentina, Alberto Fernandez ya ce, “Yau mun zama kasa ta gari da take tabbatar da ’yancin mata da kuma tabbatar da lafiyar al’umma.”

Hakan dai ya sa Alberto ya zama shugaban kasar na farko da ya halasta dokar a kasar, bayan shafe tsawon lokaci ana neman amincewar kudurin ya zama doka.

Sai dai ’yan adawa da dama a kasar sun yi sansani a wajen ginin harabar majalisar suna rokon mambobin majalisar su dakile kudurin.

Kafin wannan dokar dai, kasar ta amince da zubar da ciki ne kawai lokacin da aka fahimci akwai barazanar lafiya ga uwa mai dauke juna biyun ko kuma idan ya kasance fyade aka yi mata.