✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kaso 70 na matasan Najeriya ne ba su da aikin yi – NOA

Hakika, babu tantama wadannan sune shekarun da suka fi tasiri da amfani a rayuwar dan Adam

Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) reshen jihar Binuwai ta ce akalla kaso 70 cikin 100 na matasan Najeriya miliyan 80 ne ba su da aikin yi.

Daraktan hukumar a jihar, Richard Abimiku ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a wani taron matasa na kasa a Makurdi, babban birnin jihar.

Ya ce, “Abin da zai bugeku shine sanin cewa akwai zunzurutun matasa sama da miliyan 80 a Najeriya, wadanda kuma sune kusan kaso 60 cikin 100 na yawan jama’ar kasar.

“Ko da yake kusan kaso 70 na wadannan matasan miliyan 80 basu da aikin yi, babu tantama sune shekarun da suka fi tasiri da amfani a rayuwar dan Adam,” inji shi.

Sai dai ya ce la’akari da yawansu da kuma irin rawar da suke takawa, har yanzu matasan sun kasa yin amfani da baiwarsu wajen yin wani katabusz don ciyar da kasar gaba.

“Duk da cewa wasu matasan sun yi fice a wasu bangarorin musamman na wasanni da ilimi da kuma fasahar sadarwa da kuma dogaro da kai, har yanzu akwai bukatar a yi musu jagora ta yadda za su yi abin da ya dace,” inji shi.

Shima a nasa jawabin, shugaban Sashen Kula da Walwalar Dalibai na Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya dake Makurdi, Terhemen Aboiyar cewa ya yi duk da kalubalen da suke fuskanta, matasan Najeriya na da gagarumar gudummawar da za su iya bayarwa wajen ci gaban kasar.