✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

KASU: Limamai sun roki El-Rufai ya janye karin kudin makaranta

Malaman sun ce matsin rayuwar da iyayen dalibai suke ciki a yanzu ya wuci a yi musu karin kudi

Limaman addinin Islama sun roki Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya dakatar da karin kudin makaranta a Jami’ar Jihar (KASU).

Majalisar Limamai da Malamai ta kasa reshen jihar ta roki Gwamnatin Jihar ta yi wa Allah, ta tausaya wa halin da iyayen dalibai suke ciki su janye maganar karin kudin.

“Duba da kuncin rayuwar da iyayen dalibai suke ciki, inda suke kokarin farfadowa daga illar da kullen COVID-19 ta yi wa tattalin arzikinsu, akwai matukar daure kai a ce za a yi musu karin kudin makaranta,” inji sakon Shugaban Majalisar Limaman, Shaykh Ibrahim Nakaka, a ranar Litinin.

Ta ce, baya ga COVID-19 ayyukan da gwamnatin jihar take gudanarwa na sabunta garin Kaduna, sallamar dubban ma’aikata da ta yi ya kara jefa iyaye cikin mawuyacin hali.

A don haka ta shawarci hukumar gudanarwar KASU da Gwamnatin Jihar Kadua da su yi hattara kada su dauki matakin da zai iya jefa rayuwar matasan Jihar ta nan gaba a cikin hadari.

Ta ce yin karin kudin makaranta a halin da ake ciki a yanzu zai yi sanadiyyar cire wasu dalibai daga makarantu, wanda kuma ke iya haddasa karuwar aikata laifuka da gurbacewar tarbiyya a Jihar, “Musamman a yanzu da jihar take fama da matsalolin tsaro iri-iri.”