✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kayan masarufi sun tashi da kaso 22.79 a watan Yuni — NBS

'Yan Najeriya na ci gaba da kokawa kam tsadar kayan abinci.

Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta fitar da sabon rahoto kan sakamakon sauyi da aka samu a farashin kayayyaki a Najeriya a watan Yuni.

NBS ta fitar da sabon rahoton ne a ranar Litinin, inda ta nuna lamarin na kara jefa ‘yan kasa cikin mawuyacin hali, kamar yadda ta tabbatar a rahotonta na wata-wata da ta fitar ranar Litinin.

Hukumar ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya karu zuwa kas0 22.79 cikin 100 a watan Yuni daga kashi 22.41 da yake a watan Maris, 2023.

Rahoton ya kuma nuna cewa farashin kayan abinci ya tashi zuwa kashi 22.25 wanda ya zarce kashi 20.60 da aka samu a watan Yunin 2022.

Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur, tun a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi, ya kara jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali da dagula al’amura.

Sai dai a makon da ya gabata, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci.

Hakan na nufin gwamnatin za ta tashi tsaye wajen tabbatar da cewar abinci ya wadata a kasa da kuma saukaka wa talakawa radadin da suke ciki.

A ‘yan kwanakin nan, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan hauhawar farashin kayan abinci.