✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kisan Ummita: Kotu ta ba da umarnin tsare dan China

Kotu ta tsare dan kasar China kan badakalar kisan masoyiyarsa, Ummukulthum Buhari a Kano

Kotu ta ba da umarnin tsare dan kasar Chinan nan da ake zargi da kashe masoyiyarsa, Ummukulthum Buhari a Kano.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kano ta gurfanar da Mista Geng Quanrong a kotu mai lamba 30 da ke Titin Zungeru, kan zargin kisan matashiyar da aka fisani da Ummita, mai shekara 23.

Wanda ake zargin, mai shekara 47 ya bayyana ne a gaban kotun ne a bisa tanadin sashe na 221 na Kundin Pinal Kod.

Sai dai masu gabatar da kara, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano, sun roki kotun ta bayar da umarnin tsare shi kafin lokacin da caji zai fito don gurfanar da shi gaban kotun sama kasancewar ita kotun majistaren ba ta da hurumin gudanar da shari’ar.

Daga nan alkalin kotun, Mai sharia Hanif Khalil Yusuf, ya bayar da umarnin tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali tare da dage sauraren shari’ar zuwa 13 ga watan Oktoba, 2022.