✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kofin Duniya: Salsala da sauye-sauyensa a tarihi

Wani kare mai suna Pickles ne ya tsinto Kofin bayan an sace shi a ranar 20 ga watan Maris na 1966.

Kofin Duniya tamkar wani dunkulallen zinari da ake ba wa duk kasar da ta yi nasara a Gasar Kwallon Kafa ta tawagar kasashen duniya da ake gudanarwa duk bayan shekaru hudu.

Tun bayan soma gasar a shekarar 1930, an yi amfani da kofuna biyu: Kofin Jules Rimet Trophy daga 1930 zuwa 1970, da kuma Kofin Duniya na FIFA daga 1974 zuwa yau.

Yana daya daga cikin kofuna mafi tsada a tarihin wasanni, wanda ake hasashen darajarsa ta kai dala miliyan 20.

Kofin na farko, wanda asalin sunansa Victory wato nasara, amma daga baya aka canza masa suna don girmama shugaban FIFA na lokacin wanda kuma shi ne shugaban Hukumar Kwallon Kafar na uku a tarihi, Jules Rimet.

An dai kera kofin da zinare wanda kuma aka yi masa lullubi da azurfa da mazaunin dutsen lapis lazuli da kuma alamar tambarin Nike, wato dai manuniya ga Ubangijin Nasara da mutanen Girka suke bautawa.

Kasar Brazil a ka ba wa kofin a karon farko a shekarar 1970, la’akari da ita ce kasar da ta lashe gasar a zamanin – a shekarun 1958, 1962 da 1970.

 Asalin Kofin Jules Rimet Trophy an sace shi a shekarar 1983 kuma tun daga wancan lokaci ba a sake jin amonsa ballantana labari.

Kofin Jules Rimet  (1930 zuwa 1970)

A shekarar 1928 ne Jules Rimet ya soma shirye-shiryen samar da Gasar Kofin Duniya, inda a shekarar da ta biyo wato 1929 aka kada kuri’ar amincewa da soma gasar.

 Sunan farko da ake kiran Kofin shi ne Victory wato nasara, amma galibi ko a wancan lokaci an fi ayyana shi da Kofin Duniya ko kuma Coupe du Monde a harshen Faransanci.

Kofin Jules Rimet

A shekarar 1946 ce aka sauya wa kofin suna zuwa Jules Rimet, wanda wani masassaki dan kasar Faransa Abel Lafleur ne ya kera shi da azurfa mai lullube da zinari sanna aka yi masa mazauni da dutsen lapis lazuli.

Daga baya a shekarar 1954 aka maye gurbin mazaunin da siga mafi tsayi don a yalwata wurin rubuta bayanan duk kasar da ta lashe gasar, inda tsayinsa ya koma santimita 35 kuma nauyinsa ya tuke a kilo 3.8.

An boye kofin a kwalin takalmi

Domin tabbatar da aminci da kuma wanzuwar Kofin Jules Rimet, ya sanya aka boye kofin cikin kwalin takalmi a lokacin Yakin Duniya na biyu.

Wani dan kasar Italiya, Ottorino Barassi da ke zaman Mataimakin Shugaban FIFA, a sirrrance ya dauke kofin daga ma’ajiyara da ke ma’adanar Bankin Roma, ya kuma sanya shi cikin wani kwalin takalmi ya boye a karkashin gadonsa har sai bayan da kurar yaki ta lafa.

Kofin ya ci gaba da kasancewa a karkashin gadon Barassi har sai da aka dawo za a ci gaba da Gasar Kofin Duniya bayan Yakin Duniya na biyu a shekarar 1950 wanda Brazil ta karbi bakunci.

Barassi wanda ya taka rawa wajen ganin Italiya ta yi wa gasar masaukin baki a shekarar 1938, shi ne kuma ya rike akalar shirya gasar da aka buga a shekarar 1950.

A shekarar 1954 kuma aka maye gurbun Kofin Jules Rimet da wanda ya zarta tsayin wanda ake amfani da shi domin samun wadata wurin da ake rubuta sunayen kasashen da suka lashe kofin.

Yadda aka sace kofin

A ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1966, watanni hudu kafin Gasar Kofin Duniya da Ingila ta karbi bakunci, aka nemi kofin aka rasa yayin da ake wani bikin baje koli a Dakin Taro na Methodist da ke Westminster.

Bayanai sun ce barawon kofin kadai ya dauka ba tare da ya kula wasu hatimai ba wanda an kiyasta darajarsu ta wancan lokaci a kan fam miliyan uku.

Ma’ajiyar da aka bi aka sace Kofin Jules Rimet

Yayin da hukumomin tsaro da suka hada da na Scotland Yard suka dukufa wajen gano inda kofin Jules Rimet Trophy, kwatsam sai Joe Mears, Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta FA Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Chelsea FC da ke Landan, ya yi arba da wata wasikar neman fansa daga wani mutum da ke ikirarin sunansa ‘Jackson’.

Domin tabbatar da cewa kofin yana hannunsa, a cikin wasikar wadda Jackson ya hado ta da wani bangare na jikin kofin da akan iya cira a maida, inda ya bukaci a biya shi kudin fansa har fam dubu 15,000 kafin ya dawo da shi.

An cimma yarjejeniya haduwa da Jackson gabanin musayar kudin fansar da kuma kofin a gaban Stamford Bridge, filin wasa na kungiyar Chelsea FC.

An samu nasara har Jackson ya gabatar da kansa bayan an yaudare shi da takardun kudi na bogi, wanda wani jami’i binciken sirri ya jagoranci lamarin a matsayin hadimin Joe Mear.

Tarihi ya nuna cewa har an fara tafiya da Jackson zai jagoranci tawagar jami’an zuwa wurin da za su karbi kofin, sai ya sha jinin jikinsa cewa akwai wani abun kulla, nan take ya yi kokarin tserewa ya dira daga ana tsakar tafiya a cikin mota.

Daga karshe dai an kama Jackson, kuma bincike ya tabbatar da ainihin sunansa Edward Betchley, wanda ya saba ’yan sace-sace.

Yayin da ake titsiye shi, ya yi ikirarin cewa ba shi ne ya sace kofin ba sai dai kawai wakilci da yake yi wa wani gagararren mutum da bayyana sunansa a matsayin  ‘The Pole’.

An yanke wa Betchley hukuncin cin sarka a gidan kaso na tsawon shekaru biyu, sai dai yan sanda ba su iya gano wannan mutumin ba mai suna ‘The Pole’ wanda Betchley ya ce shi yake yi wa aiki.

Haka kuma, ’yan sandan ba su iya gano kofin ba sai bayan mako guda da wani kare ya tsinto shi a wani lambu.

Pickles: Karen da ya tsinto kofin

Yayin da aka bazama wajen neman Kofin Jules Rimet a duk fadin kasar, David Corbett, wani ma’aikacin jiragen ruwa na kamfanin Thames Lighterman, yana tsakar tafiya da wani karensa mai suna Pickles, sai ya shanshano kofin a gundumar Beulah Hilla da ke Kudu maso Gabashin Landan.

A wannan rana ta Lahadi, mako daya cif ke nan da bacewar kofin, sai David Corbett ya tsaya a wata rumfar wayar tarho domin kira, kuma a bisa al’ada ta karnuka sai Pickles mai launin baki da fari ya shiga shawagi yayin da yake jiran ubangidansa.

Can kuwa sai karen mai shekaru hudu garin shanshane-shanshane ya kwakulo kunshin wasu jarida da aka nannade da zare a karkashin daya daga cikin motocin makwabtan ubangidansa.

David Corbett da karensa Pickles wanda ya tsinto Kofin Jules Rimet

A karon farko David Corbett ya dan yi jinkiri saboda fargaba don a zatonsa bam ne aka nannade, amma daga bisani saboda ganin kwakwaf, ya warware nadin sai ya yi kacibus da Kofin

“Nan take na ruga a guje wurin mai dakina, duk da dai ita mace ce ai adawa da harkokin wasanni, amma na shaida mata cewa na tsinto Kofin Duniya, na tsinto Kofin Duniya”, a cewar Corbett yayin wata ganawarsa da jaridar Guardian.

Daga bisani Corbett ya mika kofin ga ofishin ‘yan sanda na yankin, inda aka tsare shi na wani dan lokaci bisa zargin cewa yana da hannu a satar kofin

An dai ayyana Corbett da karensa a matsayin jaruman kasa, wanda har ta kai ga Pickles ya shahara a Ingila ana haska shi a gidajen talbijin.

Bayan Ingila ta lashe Gasar Kofin Duniya karon farko a shekarar 1966, kuma daya tilo a tarihi, an gayyaci Corbett da Pickles zuwa bikin murnar lashe kofin wanda Sarauniya Elizabeth II ta mika wa Sir Bobby Moore.

Yadda Brazil ta ga samu ta ga rashi

Bayan Brazil ta lashe Gasar Kofin Duniya karo na uku a shekarar 1970, an danka wa kasar Kofin Jules Rimet a matsayin kyauta ta dindindin saboda bajintar da babu wata kasa da ta taba yin makamancinta a tarihi.

Wannan kofi dai ya subuce daga hannun kasar Brazil a shekarar 1983, bayan an sace shi karo na biyu ke nan a tarihi a hedkwatar Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil (CBF) da ke Rio de Janeiro.

Kofin na asali, an sace shi a karo na biyu a cikin 1983 daga hedkwatar Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil (CBF) a Rio de Janeiro.

Tun daga wannan lokaci ba a gano Kofin Jules Rimet ba, wanda aka yi ikirarin cewa an narkar da shi zuwa gutsattsari na zinare.

Sai dai Hukumar ta CBF a shekarar 1984 ta sanya an kera mata wani kofin makamancin wanda aka sace duk da cewa akwai banbanci a tsakaninu ta fuskar daraja.

Haka kuma, an samu cewa Hukumar FA ta kera makamancinsa bayan sace kofin da aka yi a shekarar 1997, inda ta yi wa Hukumar FIFA gwanjonsa a shekarar 1997.

Wani mai hada kayan ado a Birtaniya, George Bird ne ya sassaka wa FA kofin da zunzurutun tagulla.

Kofin Duniya na FIFA (1974 zuwa yanzu)

Kofin na yanzu, wanda ake kira Kofin Duniya na FIFA, an kaddamar da shi ne a shekarar 1974 kuma ana gabatar da shi ga duk kasar da ta lashe Gasar Kofin Duniya.

Kasashe bakwai ne suka gabatar da tayin yanayin sassakar da za a yi wa kofin, amma daga bisani aka bai wa wani mai kere-kere dan kasar Italiya mai suna Silvio Gazzaniga kwangilar aikin.

Kofin Duniya na FIFA

An kirkiri kofin da zallar zinare ma’aunin karat 18 kuma aka rubanya karfen malachite a tushensa, inda tsayinsa ya kai santimita 36.8 kuma nauyinsa ya kai kilo 6.1.

Wai kamfani a Italiya mai suna Stabilimento Artistico Bertoni ne ya sassaka kofin, inda ya kwatanta shi da siffofi biyu na mutane suna rike da Duniya.

A halin yanzu Faransa ce mai rike da kofin, wacce ta lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018, inda za ta yi kokarin kare kambunta a Gasar Kofin Duniya ta bana.

Jerin kasashen da suka lashe Kofin Duniya a tarihi

Kofin Jules Rimet:

Brazil – 1958, 1962, 1970

Uruguay – 1930, 1950

Italiya – 1934, 1938

Jamus – 1954

Ingila – 1966

Kofin Duniya na FIFA:

Jamus – 1974, 1990, 2014

Argentina – 1978, 1986

Italiya – 1982, 2006

Brazil – 1994, 2002

Faransa – 1998, 2018

Sfaniya – 2010

Jamus – 2014

Faransa – 2018