✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Ganduje daga yanke albashin ma’aikatan Kano

Ma'aikatan sun koka kan zaftare musu albashin Nuwamba da Disamba da gwamnatin jihar ta yi.

Wata babbar kotu a Kano ta dakatar da Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje daga rage albashin mambobin Kungiyar Ma’aikatan Shari’a (JUSUN) na wucin gadi.

Mambobin kungiyar ne dai suka shigar da gwamnan kara a kotu saboda zabtare musu albashin watannin Nuwamba da Disamban 2020.

Sun shigar da karar ne a ranar 5 ga Janairu 2021, ta hannun lauyansu, Barista F.I. Umar.

Da yake yanke hukuncin, alkalin kotun, Mai Shari’a Shari’a Usman Na’abba ya ba da umarnin na wucin gadi ne, inda ya kuma umarci duka bangororin biyu da su martaba yarjejeniyar da suka kulla a ranar 19 ga Disamban.

Daga nan sai ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa 28 ga watan Janairun 2021, don ci gaba da sauraronta.

Da yake tsokaci kan lamarin, shugaban kungiyar JUSUN na jihar, Muktar Rabiu Lawal, ya ce sun dauki matakin shari’a ne domin su kalubalanci rage musu albashin da aka yi.

A cewarsa, a watan Nuwamba an rage wa mambobinsu kudin da suka kai kusan Naira miliyan 41, sannan a Disamba kuma aka zaftare musu miliyan 39.

Sai dai ya ce suna fargabar kafin karshen shekara ragin albashin zai iya kai wa miliyan 300.