✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta daure ’yan majalisa saboda dukan abokiyar aikinsu

Ta mayar da martani ta hanyar jifarsa da kujera.

Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan wasu ’yan Majalisar Dokokin kasar biyu bayan samunsu da hambarar wata abokiyar aikinsu mai juna biyu.

’Yan majalisar da hukuncin ya shafa – Mamadou Niang da Massata Samb na bangaren ’yan adawa- kotun ta kuma umarci su biya Amy Ndiaye daga bangaren masu rinjaye, CFA miliyan biyar (dala 8,100.00) domin cin mutuncinta da suka yi.

A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan Majalisar Dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar.

Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki a bainar jama’a.

Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin.

To sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yadda masu shigar da kara suka bukata.

Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, an yada bidiyon harin a intanet, inda ake iya ganin Mista Samb yana tafiya zuwa wurin da Amy Ndiaye ke zaune kuma da isarsa wurin sai ya koda mata mari yayin da ake muhawara kan kasafin kudin kasar ranar 1 ga watan Disamba.

Ta mayar da martani ta hanyar jifarsa da kujera, sai dai a daidai wannan lokacin Niang ya hambare ta a ciki.

Rikici ya barke a zauren majalisar yayin da sauran mambobi suka yi kokarin kwantar da hankula.

Madam Ndiaye ’yar majalisa ce ta gamayyar jam’iyyun Benno Bokk Yakaar jam’iyyar shugaba Macky Sall.