✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ki ba da belin wanda ya mika ’yar uwarsa ga masu garkuwa da mutane

Ana dai zargin mutumin ne ga masu garkuwa don karbar kudin fansa.

Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Zariya ta ki amincewa ta bayar da belin mutumin da ake zargi da yaudarar ’yar uwarsa tare da mika ta ga masu garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

Ana dai zargin Abubakar Halliru ne da mika Binta Mohammed ga masu garkuwa da mutanen.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a Kabir Dabo, ya ce kotu ba za ta bayar da belin ba har sai an saurari shaidu tare da kallon yanayin karfinsu.

Ana tuhumar Abubakar ne karkashin sashe na 246 na Kundin Manyan Laifuka na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Dukkan lauyoyin bangarorin biyu sun bayyana wa kotun cewa a shirye suke don ci gaba da shari’ar.

Wanda ake zargin dai ya musanta aikata aikata laifin da ake zarginsa da aikatawar.

Kotun dai ta tsayar da ranakun 24 da 25 ga watan Janairun 2022 don ci gaba da sauraron shaidun bangaren masu kara.

Tunda farko dai, kotu ta ba da belin Abubakar Haliru wadda aka janye belin nasa a ranar 31 ga watan Oktoban bara, biyo bayan korafe-korafen jama’a da ya kaure a wasu kafafen yada labarai.