✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta raba auren shekara 20 kan rashin zaman lafiya

Wata Kotun Al’adu da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun na birnin Ibadan, ta katse igiyar auren da ke tsakanin wata mata da mijinta saboda rashin…

Wata Kotun Al’adu da ke zamanta a yankin Ile-Tuntun na birnin Ibadan, ta katse igiyar auren da ke tsakanin wata mata da mijinta saboda rashin fahimtar juna da ke yawan aukuwa a tsakaninsu.

Matar mutumin wacce take ’yan harkokinta na kasuwanci wadda ke zaune a yankin Amunloko-Ojuawo a Jihar Oyo, ta bayyana wa kotun cewa, mijin nata yana da taurin bashi kuma bashi da yafiya ga shi mashayin barasa.

Matar ta ce, ta yanke shawarar ganin an raba auren nasu da suka kwashe shekaru 20 saboda ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta saita masa rayuwarsa amma abun ya ci tura, inda har a wasu lokutan ta kan biya masa basussukan da ke kanshi.

“Mijina ya karar da duk abun da yake samu wurin shaye-shaye wanda hakan ya jefa ni da yaranmu cikin mayuwacin hali.”

“Mun yi kokarin sama masa aiki amma babu abin da ya fi kauna face zaman kashe wando kuma ya gaza biyan kudin hayar gidan da muke ciki na N270,000.”

“Kazalika, ya cefanar da kusan dukkan dukiyar da ya mallaka har da kayan da ke cikin gidan da suka hada da Fankoki da Jannareta da Kayan girki da Sarkar gwal dita,” in ji ta.

Shi kuwa mijin matar yayin da kotun ta neman jin ta bakinsa a zamanta da ta gudanar a ranar Talata, ya amince da a raba auren nasu kamar yadda mai dakinsa ta bukata saboda a cewarsa rashin kirkinta ya sha masa kai.

Magidancin ya bayyana wa Kotun cewa ba zai iya iyakance adadin lokutan da ya rika fito da ita daga Coci, inda a koda yaushe take fasikancin da Limamin Cocin.

“Ya mai Shari’a, ina mai tabbatar maka cewa, babban laifi na a wurin matata shi ne hana ta kwanciya da Faston da take zuwa Cocinsa a makwabtanmu.

“Mutane da dama cikin makusanta na da abokaina da muke unguwa daya da su sun sanar da ni cewa matar tawa suna soyayya sosai da Faston, sai na zuba ido har sai da na kama ta kuru-kuru.”

“Na kai kara kan lamarin zuwa kungiyar masu gidajen haya, wanda suka kirawo Limamin Cocin suka yi masa gargadi amma duk da haka abun ya ci tura.”

Bayan sauraron bangarorin biyu, Alkalin Kotun, Cif Henry Agbaje, ya katse igiyar auren saboda wannan rashin jituwa da ke tsakanin ma’auratan.

Agbaje, ya ba mijin dansu na farko, sai kuma ya bai wa matar damar ci gaba da rike ragowar yara hudun da suka haifa.

Alkalin ya kuma bawa mijin umarnin bawa tsohuwar matar tasa kudi N20,000 duk wata saboda kula da kananan yaran nasu da siya musu Abinci, ya kuma bashi umarnin daukar dawainiyar karatunsu da walwalarsu ta yau da kullum.