✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta soke belin wanda ake zargi da sassara dan makwabcinsa saboda kare

Ana dai zargin mutumin da sassara yaron saboda kare

Kotun majistare ta hudu da ke zamanta a unguwar Chediya GRA a Zariya, Jihar Kaduna, ta soke belin da ta ba Abdulmutallaib Tukur da ake zargi da sassara dan makwabcinsa saboda kare.

Kotun ya kuma tisa keyar mutumin, wanda aka fi sani da Tsalle, gidan gyaran hali saboda sassara yaron, tare da sare masa kafa da adda domin jirar shawarar lauyoyi daga Ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kaduna.

Laifin dai a cewar lauyan masu shigar da kara ya saba da sassa na 216 da 189 na Kundin shari’a na Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Tun da farko dai Mai Shari’a Dorcas Kitchener ta ba da belin wadda ake zargin ne a bisa rashin ingancin tuhumar ’yan sanda wanda suka yi a karkashin sashe na 216.

Ana dai yin shari’ar ne kan zargin da mahaifin yaron ya yi akan an sarewa dansa kafa sakamakon ya bugi wani kare da ya nufe shi a lokacin da ya dawo kiwon awaki a daji.

Da yake zantawa da yaron da aka sara, Sirajo Abdullahi Dan shekara 18, a gadon Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya, Aminiya ta gano cewa shi dan garin Tashar Zomo ne da ke Karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna.

Ya shaidawa wakilin namu cewa ya samu munanan rauni sakamakon saran shi da wani mai suna Tsalle ya yi, inda yake karbar magani a asibiti yanzu haka

Shi ma mahaifin Surajo, Malam Abdullahi Sani ya shaida wa Aminiya cewar ko da Tsalle ya gama aika-aikarsa a kan Surajo sai ya yi tafiyarsa, shi kuma sai ya tafi ofishin ’yan sanda a Giwa ya kai rahoton abinda ya faru da dansa.

Mahaifin ya ce babban abin takaicin shi ne duk da cewa suna zaune a wuri guda tun faruwar lamarin, kimanin wata biyu shi Tsalle ko wani daga iyalansa babu wanda ya je Asibiti don gaishe da Surajo, ballantana su san halin da yake ciki.

“Tun da abin ya faru mun kashe kudi fiye da Naira dubu 200 kuma a halin yanzu ana neman Naira dubu 90 domin a yi masa aiki na karshe a asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika,” inji mahaifin yaron.