✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matar da ta karya ’yar mijinta da tabarya a Sakkwato

Kotun ta bada umarnin tsare matar sakamakon samunta da laifin cin zarafi.

A ranar Laraba ne wata babbar kotun majistare ta bayar da umarnin tsare wata matar aure mai shekara 33, wadda ake zargi da azabtar da ’yar mijinta a Jihar Sakkwato.

Ana zargin matar da amfani da tabarya wajen dukan yarinyar, ’yar shekara 17, wanda hakan ya yi sanadin samun karaya a hannunta na hagu.

An gurfanar da matar a gaban kuliya bisa laifuka uku da suka hada da yin rauni, zaluntar yarinya da kuma tsarewa ba bisa ka’ida ba.

Laifukan dai sun ci karo da dokokin laifuka na Jihar Sakkwato.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeto George Idoko, ya ce an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 12 ga watan Disamban 2021, inda ake zargin matar da azabtar da yarinyar.

Lauyan wadda ake zargin, Mista Shamsuddeen Dauda, ​​ya nemi a bayar da belinta bayan musanta laifukan da ake tuhumarta da su.

Sai dai lauyan wanda suka shigar da karar ya ki amincewa da bukatar lauyan nata, saboda a cewarsa ana kan bincike.

George,  ya ce saboda sanin girman laifuffukan da kuma yanayin wadanda abin ya shafa, bada belinta na iya zama barazana.

Alkalin kotun majistaren, Fatima Hassan, ta bayar da umarnin a tisa keyar wadda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Disamba don ci gaba da shari’ar.

Kwamishiniyar kula da harkokin mata da kananan yara ta Jihar, Hajiya Kulu Sifawa, ta yabawa ma’aikatar lafiyar Jihar bisa daukar nauyin magungunan yarinyar da abun ya shafa.

Sifawa ta yi kira da a tallafawa yarinyar da abun ya shafa duba da yadda aka ci zarafinta.