✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu Ta Tsare Matar Da Ta Watsa Wa Mijinta Ruwan Zafi

Alƙaliyar Kotun, Khadijah Dauda, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu.

Wata Kotun Majistire da ke Karamar Hukumar Kontagora a Jihar Neja, ta bayar da umarnin a tsare Amina Abashe da ake zargi da watsa wa mijinta Shehu Abdullahi tafasasshen ruwa.

‘Yan sanda sun gurfanar da wadda ake zargin ce a gaban kuliya bisa laifin yi wa mijinta mummunan rauni da ya saba wa sashe na 245 na kundin dokoki shari’a.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Danladi Marafa, ya shaida wa kotun cewa matar da ake zargi ta kwarawa mijinta ruwan zafi a sakamakon wani sabani da ya shiga tsakaninsu.

Sai dai bayan karanto ƙunshin tuhumar da ake yi wa matar da ake ƙara, ta musanta aikata laifin.

Lauya mai gabatar da kara, ya bukaci da a tisa keyar matar da ake tuhuma zuwa gidan gyaran hali, domin bai wa masu ƙara damar lura da  lafiyar wanda abin ya shafa da a yanzu yake samun kulawa a Babban Asibitin Kontagora.

Ya kuma bukaci a ɗan ba su lokacin domin  tabbatar da tsaro da kare matar da ake tuhuma.

Alƙaliyar Kotun, Khadijah Dauda, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Afrilu.