✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mota ta afka wani Masallaci a Neja

Motar ta afka Masallacin yayin da jama'a suka idar sa sallar Tahajjud cikin dare.

Wata mota ɗauke da mangwaro ta afka cikin wani Masallaci yayin da jama’a suka idar sallar Tahajjud a gidan Barade da ke Karamar Hukumar Kontagora a Jihar Neja.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa jama’a sun watse daga Masallacin lokacin da lamarin ya faru.

Masallacin ya cika maƙil, yayin da jama’a ke tsaka da addu’o’i a goman ƙarshe na watan Ramadan.

Majiyar ta ce ɓangaren da abin ya shafa na masallacin, shi ne inda mata da ƙananan yara ke yin sallar Tahajjud.

Direban motar ya taso ne daga garin Bida na Jihar Neja, inda ta nufi Sakkwato da fasinjoji hudu, lokacin da motar ta ƙwace ya afka kan Masallacin da ake sallar Tahajjud.

Ɗaya daga cikin motocin da aka ajiye a wajen Masallacin, motar ta yi awon gaba da ita.

Wani mazaunin garin, Yahaya Suleiman, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne minti shida bayan masallatan sun kammala sallar.

“Mun gode wa Allah. Wajen da motar ta kutsa ciki ɓangaren mata da yara ne. Jama’a sun idar da sallar Tahajjud sun watse lokacin da lamarin ya faru. Ba a rasa rai ba amma motar ta yi wa Masallacin ɓarna,” in ji shi.

Ɗaya daga cikin fasinjojin da ke bayan motar mai suna Mustapha Sakkwato, ya bayyana cewa yana tsaka da barci sai ganinsa ya yi a ƙasa.

“Lokacin da lamarin ya faru, barci nake yi. Sai ganin kaina na yi a ƙasa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asuba.

“Mun tashi daga Bida, mun nufi Sakkwato. Mu biyar ne a cikin motar; babu wanda ya samu rauni. Masu kayan suna cikin motar tare da direban. Ban san abin da ya faru ba saboda ina barci a bayan motar,” in ji shi.